Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 05 11Article 450720

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Bayern Munich ta lashe Bundesliga sau 9 a jere

Gwarzuwar gasar Bayern Munich  ta kara lashe gasar karo na tara a jere Gwarzuwar gasar Bayern Munich ta kara lashe gasar karo na tara a jere

Gwarzuwar gasar Bayern Munich ta kara lashe gasar karo na tara a jere.

Wannan na zuwa ne bayan rashin nasarar da RB Leipzig da ke biye mata ta yi a hannun Borussia Dortmund da ke neman tikitin zuwa Champions a badi.

Leipzig, wadda ta fara jan ragamar gasar da maki bakwai akan Munich an doketa 3-2.

Dan wasan Ingila Jadon Sancho ne ya ci kwalo biyu bayan Marco Reus ya fara jefa daya.

Da kwallayen Luka Klostermann da Dani Olmo wasan ya zama 2-2 kafin daga bisani kwallon Sancho ta karshe ta bai wa Munich damar cin gasar gabanin wasanta da Borussia Monchengladbach.

A watan Afrilu, Bayern ta sanar da shirinta na daukar kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann, wanda zai sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar da kungiyar.

Wannan na zuwa ne bayan da kocinta na yanzu Hansi Flick ya sanar da cewa ba zai ci gaba da horas da kungiyar ba.

A gefe daya kuma Dortmund ta koma ta hudu a teburi wanda hakan zai bata damar samun gurbin Champions a shekara mai zuwa.