Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 04 13Article 450183

BBC Hausa of Mardi, 13 Avril 2021

Source: BBC

Inter na bukatar maki 16 domin ta lashe Serie A na bana

Tsohon dan wasan Manchester United, Matteo Darmian shi ne ya ci kwallon tilo Tsohon dan wasan Manchester United, Matteo Darmian shi ne ya ci kwallon tilo

Inter Milan ta yi nasarar cin Cagliari 1-0 a wasan mako na 30 a gasar Serie A da suka fafata ranar Lahadi.

Tsohon dan wasan Manchester United, Matteo Darmian shi ne ya ci kwallon tilo, saura minti 13 a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Inter ta yi nasara a wasa 11 a jere a gasar ta Italiya ta kuma ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki 11.

Inter wadda Antonio Conte ke jan ragama na bukatar maki 16 nan gaba daga sauran karawa takwas da ta rage a wasannin Serie A ta bana.

Rabon da Inter Milan ta lashe kofin gasar Italiya tun kakar 2009/10.

AC milan ce ke mataki na biyu a kan teburin Serie A mai maki 63 da tazarar maki daya tsakaninta da Juventus wadda ta doke Genoa a wasan mako na 30 ranar Lahadi.

Juventus wadda take ta uku a teburi da tazarar maki 12 tsakaninta da Inter, ita ce mai rike da kofin Serie A, kuma na tara da ta lashe a jere.