Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 03 12Article 449613

BBC Hausa of Friday, 12 March 2021

Source: BBC

Sudan ta yi wa kwamandan ƴan tawaye afuwa

Mista Hilal ya kasance kusa da tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir Mista Hilal ya kasance kusa da tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir

Sudan ta saki wani shugaban mayaƙan sa kai mai karfin faɗa a ji wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya wa takunkumi kan zargin aikata munanan ayyuka a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.

Afuwar da aka yiwa Musa Hilal, shugaban rundunar Janjaweed, ta biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu a kai, a watan Oktoban da ya gabata tsakanin gwamnatin riƙon ƙwaryar Sudan da ƙungiyoyin ƴan tawayen Darfur.

Mista Hilal ya kasance kusa da tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir amma ya samu saɓani da shi kuma aka cafke shi a shekarar 2017.

Kimanin mutum 300,000 aka kashe sannan mutane miliyan 2 da rabi suka rasa matsugunansu a tsawon shekaru na rikici a Darfur, yawancinsu tsakanin Larabawan Janjaweed da al'ummomin Afirka.