Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 03 06Article 449511

BBC Hausa of Saturday, 6 March 2021

Source: BBC

Gwamnatin Kano ta ce ta gamsu da hana yin muqabala da Sheikh Abduljabbar

Sheikh Abduljabbar (hagu) da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje Sheikh Abduljabbar (hagu) da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Gwamnatin Kano ta bayyana gamsuwa da hukuncin da wata kotun majistre a jihar ta yanke na hana yin muƙabala, wato zaman tattaunawa da fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake jihar Sheikh Nasiru Kabara.

Ranar Jumma'a ne kotun ta yanke wannan hukunci, kasa da sa'a 48 kafin gudanar da muƙabalar da aka jima ana jira.

Hukuncin ya buƙaci a tsaya a kan hukuncin da kotun ta yanke tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya haɗar da haramtawa Sheikh Abduljabbar yin wa'azi a jihar ta Kano.

Yayin wata zantawa da BBC, kwamishinan watsa labarai na Kano Muhammadu Garba, ya ce bayan tattaunawa da gwamnati ta yi da ma'aikatar shari'a, sun gamsu da wannan hukunci, don haka an fasa yin muƙabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadin nan.

BBC ta tambaye shi a kan zargin da wasu ke yi na cewa gwamnatin Kano na da hannu a shigar da ƙarar da aka yi don hana wannan zama, saboda yadda sarkin Musulmi ya ce baya goyon bayan a yi shi, inda ya ce kwata kwata wannan zargi ba gaskiya bane.

Ya ƙara da cewa ko da an ɗaukaka ƙara daga baya wata kotun ta ce a gudanar da zaman, sai gwamnatin Kano ta sake yin karatun ta-nutsu tukunna kafin duba yiwuwar yin hakan.

Me Sheikh Abduljabbar ya ce a kan hukuncin ?

Ɗaya daga cikin lauyoyin dake kare Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara a shari'ar Barista Rabiu Shu'aibu Abdullahi, ya ce su a iya saninsu wannan zama yana nan daram, domin babu wani waje da kotun ta fito ta ce ta hana yin Muƙabala ƙarara.

''Abun da muka fahimta da wannan hukunci shine kotu ta ce a ci gaba da aiki da hukuncin da ta yanke na ranar 8 ga watan Fabrairu. na cewa ta hana Malam Abduljabbar yin wa'azi da kuma furta kalaman tunzuri, da rufe masallacinsa da cibiyarsa, babu wani waje da tace kada a yi muƙabalar da aka shirya.

Ya ƙara da cewa kwata kwata takardar hukuncin da kotu ta yanke bashi da alaka da yin muƙabalar, ballantana a ce za a fasa yin zama.

Barista Rabiu ya ce ko da wasu na son fakewa da hana Malam Abduljabbar yin wa'azi da kotu ta yi, ''to a sani cewa ba wa'azi za a yi da Malam ba, ita gwamnatin Kano cewa ta yi tattaunawa za a yi''

Matashiya

Ranar 4 ga watan da ya wuce na majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar, saboda furta kalaman tunzuri a yayin wa'azi da kuma kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

A wannan lokaci gwamnatin ta shaidawa BBC cewa ta tsaya ta yi nazari, kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, har akwai rahotanni daga wajen manyan malamai da kuma hukumomin tsaro game da kalaman da malamin ke furtawa, shi ya sa ta dauki wannan mataki.

Tun a wannan lokaci ne gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike a kan wadannan zarge zarge, amma har yanzu bai gamatar da rahotonsa ba.

Shi dai Malamin ya yi zargin cewa gwamnatin Kano bata yi masa adalci ba wajen daukar matakin ba tare da an ji daga nasa bangaren ba, inda ya nemi a shirya masa zama da malaman dake ƙalubalantarsa domin ya kare duk abin da yake faɗi, buakatar da gwamnatin ta amince da ita, kafin daga bisani kotu ta haramta yin zaman kasa da awanni 48 kafin a gudanar da shi.