Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 03 16Article 449675

BBC Hausa of Mardi, 16 Mars 2021

Source: BBC

Wadanda za su yi wa Real wasa da Atalanta a Champions League

Real ta ziyarci Atalanta ranar 24 ga watan Fabrairu a wasan farko Real ta ziyarci Atalanta ranar 24 ga watan Fabrairu a wasan farko

Real Madrid za ta karbi bakuncin Atalanta a wasa na biyu a Champions League ranar Talata a Alfredo Di Stefano.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin za su fafata a gasar ta Zakarun Turai a tsakaninsu, kuma Real na sa ran lashe kofin nan, bayan da aka fitar da ita a Copa del Rey aka karbe Spanish Super Cup.

Real ta ziyarci Atalanta ranar 24 ga watan Fabrairu a wasan farko na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar, inda ta ci 1-0, kuma Ferland Mendy ne ya ci mata kwallon.

Real tana ta uku a teburin La Liga na bana da maki 57 da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona ta biyu, bayan da Atletico ce ta daya mai maki 63.

Tuni kuma kocin Real, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su fuskanci Atalanta a ranar ta Talata.

'Yan wasan Real Madrid su 19:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallaye: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da Rodrygo da kuma Hugo Duro.