Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 05 30Article 451063

BBC Hausa of Sunday, 30 May 2021

Source: BBC

Shugaban Faransa ya yi barazanar janye dakarun kasar daga Mali - Amma me yasa haka?

Emmanuel Macron, shugaban Faransa Emmanuel Macron, shugaban Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi gargadin cewa ƙasarsa za ta janye dakarunta a Mali, idan har rikicin siyasa a ƙasar ya ƙara haifar da tsattsauran ra'ayin Islama.

Wannan na zuwa bayan sake yin juyin mulki sau biyu cikin wata tara a ƙasar da ke yammacin Afirka.

Kalaman na Mr Macron an wallafa su a mujallar du Dimanche, inda aka yi hira da shi kan manufar Faransa kan kasashen Afirka.

Shugaban Macron ya yi gargadin cewa akwai hadari ganin yadda Mali ke karkata zuwa ga masu tsattauran ra'ayin Islama.

Faransa wadda ke kan gaba wajen yaki da masu ikirarin jihadi na da sojoji 5,100 a Mali da ke yankin Sahel.

Dakarun Faransa na aikin taimakawa sojojin kasashen Mali da Mauritania da Nijar da Burkina Faso da Chadi domin kakkabe 'yan bindiga a yankin Sahel tun 2013.

Da ya ke magana akan Mali, Macron ya ce ya shaida wa shugabannin yankin cewa Faransa ba za ta taɓa taimakon duk wata kasa da ke wasa da mulkin dimukradiyya ba kuma kasarsa ba ta da burin barin dakarunta a Afrika har abada.

Sama da shekaru 20 Faransa na samar da taimakon soji domin ba da kariya ga shugabannin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka, tana yawan aika sojojinta ko kuma kai hare-haren sama domin yaki da masu tayar da kayar baya.

Meke faruwa ne a Mali?

Kotun tsarin mulki ta kasar ta bayyana shugaban sojojin da suka yi juyin mulki kanar Assimi Goïta a matsayin wanda zai jagoranci mika mulki ga farar hula, kwana biyu bayan ya ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya.

Ya kare matsayarsa ta hambarar da Shugaba Bah Ndaw da Firaiministansa Moctar Ouane a matsayin wani abu da ya zama dole, saboda sun kasa gudanar da aikinsu yadda ya kamata, kuma suna yin zagon kasa ga shirin mika mulki ga farar hula a nan gaba.

Sojoji ne suka kama mutanen biyu suka tsare su, bayan nadin mukarraban da aka yi wanda Kanar Assimi Goïta ya ce ba a tuntube shi ba aka gudanar.

Shi ne ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen shugabancin Ibrahim Boubacar Keita.

Kanar Assimi Goïta ya yi alkawarin cewa za a nada Firaiminista a cikin 'yan kwanaki, kuma a gudanar da zabe a shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara.

A gefe guda kuma, shugabannin yankin za su gudanar da wani taro a ranar Lahadi na "tuntubar" juna a Ghana, wanda ake sa ran Kanar Assimi Goïta ya halarta.

Me ya sa Mali taki dawowa hayyacinta?

Yana da wahala a samar da sauyi cikin sauki - bugu da kari ga kasar ba ta da arziki, kuma yankuna da dama babu ci gaba.

Wani juyin mulki da aka yi a 2012 ya haifar da rikicin masu ra'ayin kishin Islama, hakan ya sa suka kwace iko da arewacin kasar.

Daga baya dakarun Faransa suka taimaka aka kara kwace yankin, amma an ci gaba da kai hare-hare wanda ya haifar da rashin alkiblar siyasa a yankin.

Wannan ya haifar da rashin kwarin gwiwa kan shugabannin sojin da suka gaza kawar da masu ikirarin jihadi, wadanda ayyukansu suka fantsama kasashen da ke makwabtaka na Burkina Faso da Nijar.