Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 04 19Article 450310

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Super League: Me ya sa manyan kungiyoyin kwallon kafa suke son kafa sabuwar gasa?

Kungiyoyin kwallon kafa 12 ne suka amince su kafa sabuwar gasa ta European Super League Kungiyoyin kwallon kafa 12 ne suka amince su kafa sabuwar gasa ta European Super League

Arsenal, Chelsea, Liverpool, Manchester City, Manchester United da Tottenham na daga cikin kungiyoyin kwallon kafa 12 da suka amince su kafa sabuwar gasa ta European Super League ko ESL a takaice.

A wani mataki da kungiyoyin kwallon kafar Turai suka dauka, kulob-kulob na Firimiya League za su hade da AC Milan, Atletico Madrid, Barcelona, Inter Milan, Juventus da Real Madrid.

Wadanda za su kafa sabuwar gasar ta ESL sun ce kulob-kulob din da za su daukin nauyinta sun amince su samar da "gasar wasa ta tsakiyar mako", yayin da sauran kulob-kulob za su ci gaba da yin wasanninsu kamar yadda suka saba.

Kungiyar ta ce tana da aniyar kaddamar da kakar wasan da ta ce za a fara ba tare da bata lokaci ba, tare da cewa suna sa ran kulob uku za su shigo ciki nan ba da jimawa ba.

ESL ta kara da cewa suna shirin kaddamar da gasar wasan kwallon kafar mata da zarar an kammala wasannin maza.

Sai dai firaiministan Birtaniya Boris Johnson da Ueafa da kuma Firimiya League sun yi allawadai da matakin, a lokacin da aka yi sanarwar a karshen mako.

A baya hukumar kwallon kafar duniya ta FIFA, ta ce ba za ta amince da irin wannan gasar ba, sannan 'yan wasan da suka shiga cikin shirin ka iya rasa damarsu ta buga wasan kwallon kafar duniya baki daya.

Ita ma hukumar kwallon Turai ta Uefa ta jaddada gargadi a ranar Lahadi cewa za ta kori 'yan wasan da suka shiga sabuwar kungiyar daga buga wasannin turai ko ma na duniya baki daya, sannan za a hana su wakiltar kasashensu a lokacin gasar cin kofin duniya.

Bayan sanarwar da Super League ta yi, hukumar Fifa ta nuna rashin amincewa da ita tare da kiran dukkan kungiyoyin da ke ciki da suka tayar da jijiyoyin wuya da su kwamtar da hankalinsu tare da tayin sasantawa domin ci gaban kungiyoyinsu.

A wata sanarwa da ESL ta fitar ta ce: "Kulob-kulob din da za su dauki nauyin wasannin za su tattauna da hukumomin Uefa da Fifa, domin aikin hadin gwiwa da zai samar da ingantacciyar sabuwar kungiyar da kawo ci gaba a duniyar tamaula baki daya."

Me ya sa yanzu?

An yi wata tattaunawa a watan Oktobar bara da ta hada da bankin JP Morgan, a kan sabuwar gasar da za ta lashe kusan fam biliya bakwai, wadda za ta maye gurbin gasar Zakarun Turai.

Uefa tana fatan shirin sabuwar kungiyar Zakarun Turai, wadda za ta kunshi kungiyoyi 36, zai kawo sauye-sauyen da ake son gabatarwa a ranar Litinin, kafin samar da kungiyar Super League.

Sai dai kulob-kulob 12 da ke cikin Super League suna ganin sauyin ba shi da wani tasiri sosai.

Sun ce annobar korona da duniya ke fama da ita, ta janyowa tattalin arzikin hukumar kwallon kafar turai yana tangal-tangal da rashin tabbas.

Sun kara da cewa "A watannin da suka gabata, an yi zazzafar tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fagen tamaula kan makomar ci gaban wasannin Turai."

"Kulob-kulob sun amince matakan da ake ganin za su magance matsalar da aka tattauna a kai a wajen taron ba su tabo manyan batutuwa ba, ciki har da bukatar samar da manyan wasanni masu inganci, da karin kudaden shiga ga daukacin wasannin kwallon kafa."

  • Real Madrid ta kasa samun maki uku a Getafe
Yaya aka tsara batun?

Gasar za ta kunshi kungiyoyi 20 - mambobi 12 da za su kafa ta tare da kulob uku da ba a fadi sunayensu ba da kuma ake sa ran za su shiga tsarin nan ba da jimawa ba, da bangarori biyar da duk shekara za su samu nasarar shiga gasar bisa kokarin da suka yi daga kasashensu.

Karkashin tsarin, ESL za su fara wasanni a watan Agustan kowacce shekara, inda za a dinga yin wasannin a tsakiyar mako, za kuma a dinga raba kulob-kulob zuwa rukuni biyu mai 'yan wasa 10, da za su rika buga wasa a ciki da wajen kasashensu.

Uku daga cikin kowacce kungiya za su kai bantensu zuwa gab da na kusa da na karshe, yayin da wadanda suka zo na hudu da na biyar za su buga sauran wasannin.

Daga nan za a ci gaba da bin tsarin da ake yi na wasan Champions League, kafin su buga wasan karshe a watan Mayu.

ESL ta ce za ta samar da kudade fiye da wanda ake samarwa na gasar Champions League, za kuma a samar da ingantaccen sakamako da samar da kudaden shiga a baki dayan wasannin da za a yi.