Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 05 01Article 450512

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Abubuwa biyar da suka kamata ku sani game da sabunta Apple iOS 14.5

Apple ya samar da sabbin hotunan da ake amfani da su wurin sadarwa Apple ya samar da sabbin hotunan da ake amfani da su wurin sadarwa

Apple ya sanar da fitar da sabuwar babbar manhajarsa ta iOS 14.5 a wayar salula ta iPhone da kuma iPad.

Manhajar za ta bai wa mutum zabi idan yana son kamfanoni su sani a lokacin da yake amfani da shafukan sada zumunta.

Amma ga wasu abubuwan da suka ja hankalinmu.

Bude waya fuska a rufe

Abin da aka sani shi ne wayoyin hannu na zamani na da fasahar da ke amfani da fuska wurin bude waya.

To a wannan sabuwar babbar manhaja ta iOS 14.5 mutum kan iya bude wayarsa ko da kuwa ya rufe fuskarsa baki daya.

Baya ga waya, za a iya amfani da wannan fasaha wurin bude agogon hannu da ake kira Apple Watch.

A sanarwar da Apple ya fitar ya ce: "Matsawar kana sanye da agogon Apple Watch, za ka iya kallon wayarka ta iPhone kuma a take za ta bude, yayin da agogonka zai fada maka cewa wayarka ta bude."

Wato abin nufi a nan shi ne idan mutum yana so wayarsa da agogonsa za su rika aiki tare. Ko kuma za ka iya bude wayarka ta hanyar kallon agogonka.

Manhajar da ke sa kamfanoni da ke kan waya izini

Haka kumma sabon iOS din ya zo da wata manhaja da za ta ba mai amfani da iPhone zabi idan har yana so wata manhaja, misali Facebook ya samu bayani a lokacin da kake kan intanet (wato online) ko kuma a'a.

Wannan manhaja ce ta haifar da ce-ce-ku-ce, don a baya sauran manhajoji kamar Facebook na amfani da cewa mutum na onlayin sai su tura masa talla ta hanyar bibiyar abubuwan da ka fi sha'awa a intanet. A yanzu kuma sabon iOS 14.5 ya ba da zabi.

A kan haka kamfanin Facebook ya fito fili ya nuna adawa da wannan manhaja.

Sai dai masana na zargin Apple da nuna son kai.

Dalili kuwa shi ne kamfanoni na samun kudade wurin tallace-tallace da suke karba, kuma idan har hakan ba ta samu ba to kuwa za su fara sayar da manhajojinsu wanda hakan zai sa Apple ta samu makudan kudi.

Sabbin Emojis

Baya ga manhajojin, Apple ya samar da sabbin hotunan da ake amfani da su wurin sadarwa ko kuma nuna yanayin da mutum ke ciki da ake kira emojis.

Daga cikinsu akwai fuskar da ke nuna cewa ana mura, da kuma zuciya mai ci da wuta da kuma mace mai gemu da dai sauransu.

Manhajar Siri

Apple ya kuma sanar da ƙara inganta manhajarsa ta 'Siri' wata murya da masu amfani da Apple ke iya sakawa aiki a wayarka.

A sabon iOS Apple ya ba masu amfani da wayarsa zabin muryar da suke so su ji a 'Siri', sabanin a baya da murya daya ce kawai.

Apple ya ce ya yi wannan sauyi ne la'akari da cewa ya kamata a bai wa jama'a zabin irin muryar da suke so su ji a wayoyinsu.

Amma masu suka sun ce duk da a China Apple ke kera kayansa, kamfanin bai taba fitowa ya soki cin zarafin da gwamnatin kasar ke yi wa yan ƙabilar Uighur ba.

A kan haka masu sukar suka ce ya kamata Apple ya riƙa yin allah-wadai a gida da waje ba tare da nuna bambanci ba.

AirTags

AirTags ita kuma wata na'ura ce da za ta iya gano wa mutum kayansa da suka ɓata.

Za ka iya maƙala wannan ƴar ƙaramar na'urar da ke kama da zobe a jikin makulli ko jaka ko wani kaya mai muhimmanci, saboda ka iya gano inda suke da zarar sun ɓata.

Amma wannan na'ura ta Apple AirTag na kamanceceniya da wata irinta da ke kasuwa mai suna 'Tile'.

Ko a makon da ya gabata majalisar dattawan Amurka ta zargi Apple da satar fasahar 'Tile'.

Ita ma shugabar kamfanin na Tile Kirsten Daru ta sanar cewa "muna maraba da takara a harkar kasuwanci, amma kuma ya kamata ta zama tsabtatacciyar takara ba irin yadda Apple ya yi ba a wannan karon. Hakan bai dace ba."

To amma Apple ya mayar da martani cewa bai saci fasahar Tile ba, kuma na'urarsa ta AirTag kwata-kwata ba ta kama da komai a kasuwa, a cewar Kyle Andeer na kamfanin Apple.