Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 04 30Article 450494

BBC Hausa of Vendredi, 30 Avril 2021

Source: BBC

Man United ta fara jin kanshin kofin Europa League

Manchester United ta yi nasarar caskara Roma da ci 6-2 a wasan zagayen farko Manchester United ta yi nasarar caskara Roma da ci 6-2 a wasan zagayen farko

Manchester United ta yi nasarar caskara Roma da ci 6-2 a wasan zagayen farko na daf da karshe a Europa League da suka fafata ranar Alhamis a Old Trafford.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Bruno Fernandes a minti na tara da fara tamaula, sai dai Roma ta farke ta hannun Lorenzo Pellegrini a bugun fenariti.

Saura minti 11 su yi hutu ne Roma ta kara na biyu ta hannun Edin Dzeko.

Minti biyu da komawa zagaye na biyu ne Edison Cavani ya farke kwallo, sannan ya kara na biyu a ragar Roma.

United ta kara cin na hudu ta hannun Bruno Fernandes a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma na biyu da shima ya zura a raga a fafatawar.

Bruno Fernandes ya zama dan wasan Manchester United na uku da ya ci fenariti 20 ko fiye da hakan, bayan Ruud van Nistelroy mai 28 da Wayne Rooney mai 27 a raga.

Saura minti 15 a tashi daga wasan Paul Pogba ya kara na biyar a raga, sannan Mason Greenwood ya ci na shida.

Ranar Alhamis 6 ga watan Mayu za a buga wasa na biyu, inda Manchester United za ta ziyarci Roma a gasar ta Europa League.