Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 05 04Article 450589

BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: BBC

Ramadan: Hotunan yadda masu sana'ar ƙarfi ke neman abinci a lokacin azumi

A mafi yawan lokuta ana gudanar da azumin watan Ramadan ne a Najeriya a lokacin zafi.

A wannan shekarar ma 'yan Najeriya, musamman wadanda ke zaune a arewacin kasar, suna fama da zafi a lokacin azumi.

Hakan ya sa a lokuta da dama za ka ga masu aikin ƙarfi na neman abinci cikin zafin rana.

Yayin da ake shirin shiga kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan, mun kawo muku jerin hotunan yadda al'ummar musulmi a Najeriya da ke aikin ƙarfi ke neman abinci da azuminsu a baki.



Wasu matasa ke yanka katako kafin buɗe baki



Anan wani mutum ne yake tura kurar ruwa yana neman masu saye wataƙila don su yi aikin abincin buɗe baki a birnin Kano...



Wadannan masu sana'ar sayar da ruwan baron suna tallan ruwan da tsakar rana



Matsashi na aikinsa na kafinta da tsakar rana



Wani yaro da ke sana'ar jari-bola da tsakiyar rana.