Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 04 27Article 450449

BBC Hausa of Tuesday, 27 April 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ronaldo da Sima da Varane, Nagelsmann da Shaqiri

Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus

Paris St-Germain ta yi wa Manchester United zara a yarjejeniyar da suka gabatar na neman daidaitawa da ɗan wasan gaba, Cristiano Ronaldo, mai shekara 36 da ke taka leda Juventus. (Tuttosport - in Italian)

Manchester United na bibbiyar ɗan wasan gaban Slavia Prague asalin Senegal, Abdallah Sima, mai shekara 21. (Manchester Evening News)

RB Leipzig ta nemi euro miliyan 25 (£21.7m) daga Bayern Munich kafin cimma yarjejeniya da ita kan kocinta Julian Nagelsmann (Sky Sports)

Kocin Ajax Eric ten Hag zai shiga jeren mutane da Tottenham ke fatan maye gurbin Nagelsmann da Bayern ke shirin dauke wa. (Telegraph)

Kocin Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 22, zai ci gaba da zama a AC Milan duk da cewa kwantiraginsa zai kare a wannan kakar da kuma tayin da ya samu daga Manchester United da Chelsea. (TalkSport)

Real Madrid ba za ta dage a kan ci gaba da rike Raphael Varane ba, mai shekara 28, da ake alaknatawa da Manchester United da Chelsea. (AS - in Spanish)

Ɗan wasan gaba a Swiss Xherdan Shaqiri, mai shekara 29, na son yin adabo da Liverpool a wannan kakar. (Football Insider)

Arsenal ta shiga tattaunawa da ɗan wasan Ingila Emile Smith Rowe, mai shekara 20, kan sabon kwangila. (The Athletic - subscription required)

Kulon din ya shirya sayer da ƴan wasan hudu a wannan kakar domin cike gibin sabbin kwangilar da zai shiga. (Football London)

Chelsea da Manchester United sun zura ido kan ɗan wasan Brighton Andrew Moran, ɗan shekara 17. (Team Talk)

Barcelona na da ƙwarin-gwiwar cewa Eric Garcia, mai shekara 20, zai koma ƙungiyar idan kwantiraginsa da Manchester City ya ƙare a wannan kakar. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Roma ta zaɓi tsohon kocin Chelsea da Juventus, Maurizio Sarri, a matsayin sabon kocinta a sabuwar kaka. (Corriere dello Sport - in Italian)

Leeds ta shirya shiga tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Northern Ireland, Stuart Dallas, kan sabuwar yarjejeniya (Football Insider)

Sabon kulob din da ya tsallake zuwa Championship, Norwich na farautar Robert Andrich, ɗan kasar Jamus mai shekara 26 wanda yanzu haka ke taka leda a Union Berlin. (Bild via Norwich Evening News)