Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 05 17Article 450828

BBC Hausa of Monday, 17 May 2021

Source: BBC

Israel-Gaza: Abin da doka ta ce a kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa

Rikici tsakanin Hamas da Isra'ila ta barke a mokonnin baya Rikici tsakanin Hamas da Isra'ila ta barke a mokonnin baya

Dokar kasa da kasa ta zayyana yadda kasashe za su yi amfani da karfi lokacin rikici.

Kusan a ko wanne rikici da ake samu akai-akai, akan samun mahawara kan kamatan da za bangarorin biyu za su dauka da suke kan doron doka - tsakanin Isra'ila da Hamas.

Matakin kare kai

Kamar a baya hare-haren da Isra'ila duka ta kai ta ce ta kai su ne a matsayin matakin kare kai.

Kamar yadda yake a tanadin doka na 51 na Majalisar Dinkin Duniya, 'yan cin kare kai wani abu ne na wajibi a cikin dokokin duniya. Duk da cewa dai ana yawan kai ruwa rana kan wannan bangare na dokar. sai dai a ko ina an yarda kasa ta kare kanta daga harin da za a kai mata na makamai.

Amma kuma akwai muhawara kan yawan harin da za a kai kan kasa ta dauki matakin kare kanta. Yawancin lauyiyin duniya sun yarda cewa harin roka kan fararen hula da zai iya lalata rayuwarsu ya fada karkashin tanadin doka ta 51.

Amma lamarin kare kai a rikici abu ne da kullum yake janyo ce-ce-ku-ce. Bangarorin da ke rikici na da wahala su amince kan cewa wane ne ke kai hari wane kuma na kare kansa - rikicin Isra'ila da Falasdinawa na fuskantar wannan ja-in-ja. Amma a wannan gabar, masu sukar Isra'ila na kawo hujjoji biyu.

Na farko, sun ce matakin kare kai yana zuwa ne lokacin da ake rikici takanin kasashe biyu, amma ba wani yanki ba da ba a ayyana a kasa ba kamar Gaza. Sai dai kasashe da yawa na ja da wannan maganar musamman tun bayan kai harin 11 Satumba 2011, amma hurumin kotu mai yanke hukunci akan wannan batu ba.

Na biyu kuma shi ne, Kamar kwamitin ba da agaji na duniya Red Cross na daga cikin wadanda ke kallon Gaza a matsayin wadda ke karkashin mamayar Isra'ila saboda yanayin ikon da Isra'ila ke da kan yankin.

Amma Isra'ila ta dage cewa ba ta mamaye Gaza ba, tun da ta fice daga yankin a 2005 tana cewa babu yadda za ta iya mamaye shi ba tare da isassun dakaru ba.

Lamarin matakin kare kai a bude yake. Dokar kasa da kasa ta bai wa kasashen damar kare kansu idan halain hakan ya samu, amma sai da sojoji.

Ana gaza fahimtar manufar kare kai wasu sai su ce, ido a madadin ido, makamin roka daya a madadin irinsa. Amma ba haka abin yake ba: babu wani wuri da aka yi bayanin amfani da soji domin daukar fansa.

Dokar rikicin makamai

Matakin kare na dokar kasa da kasa ce da ke tafiyar da amfani da dakaru ko kuma "afkawa cikin yaki"(na koma wa ga wata kalmar Latin Amurka jus ad bellum wanda hakan ke nufin "dokar yaki").

Wani bangare na daban a dokar da ta yi magana kan rikici idan an fara shi. Ana kiranta dokar makamai a lokacin yaki.

Ana amfani da wannan dokar ne a lokacin da aka ayyana rikicin a matsayin na makamai, tare da wasu tanade-tanade da ke tafiyar da kasashen duniya da kuma dokar amfani da makamai lokacin rikici.

Ana amfani da wannan dokar ne ba tare da lura da dalilan da suka kai bangarorin da ke rikici da juna ba suka fara amfani da soji.

Don kasa ta fi gaskiya a farkon yaki kamar yadda doka ta ce, baya nufin yancin da kai hari kan makiya. Zai iya yiwuwa kasar da ke tafiya bisa doron doka ta aikita wani abu da ya sabawa dokar yaki da makamai - haka itama dayar.

Dokar amfani da makamai lokacin yaki ta yi bayani daki-daki kan bangarori da yawa wadanda suka hadar da kare fararen hula, yadda za a yi da fursunonin yaki da da kuma yadda ya kamata a mamaye yankuna, duka wadannan an yi su ne domin kare bangare hudu da suka hadar da: Hakkin dan adam da kuma amfani da sojoji idan ya zama dole da kuma banbanci da kaso.

Hakkin dan adam da amfani da sojoji idan ya zama dole

Dokar hakkin dan adam na bukatar sassauta fushi domin kaucewa mafisa da kuma azabatarwa.

Of course, the fact that the law permits a certain action does not make it wise in a political, moral or strategic sense.

A ko wanne irin yanayi, ba za a iya kare daukar matakin soji ba a wurin da aka haramta amfani da shi a doka.

Banbanci da samun kaso

Wani bangare na dokar yaki da makamai shi ne banbancewa: dole bangarori biyun da suke yaki da juna su banbance tsakanin soji da fararen hula a kowanne lokaci.

Mabanbanta hujjoji sun yi karin bayani kan wannan bangaren dokar. An haramta kai hari kan fararen hula da kayayyakinsu. An yarda akai hari kan dakaru ko kuma masu taimaka musu ko da ba kai tsaye ba, haka kuma da duk wani mallaki na sojoji.

Wannan bangaren da ke maganar banbancewa ya haramta yin barazana a cikin fararen hula da nufin neman wani dan ta da kayar baya, da kuma kai hari a fakai ce da nufin kai wa kan kayayyakin soji. Kamar harin da aka kai kudancin Isra'ila gaba dayansa ya saba da wannan doka.

Amma yaushe ne irin wannan harin yakan zama halastacce?

Dokar kasa da kasa ta yi bayani kan abin da ake kira kayayyaki mallakar soji, "sune kayan da ke bayar da gudunmawa wajen yaki..... "

Bangaren Isra'ila da kuma na Hamas sun fada wannan tsari. Matsaloli na karuwa kan abin da ake kira harin bangarori biyu - Kamar yadda Nato suka ruguwa gidan talabijin na Sabiya a 1999 a yakin Kosovo.

Wani abu mai wuyar sha'ani shi ne yadda ake girke kayan yakin soji kamar su roka da wajen ajiyar harsashi a kusa da farern hula ko kuma inda kayan fararen hlar suke. Kusan duk wani hari da za a kai a yankin da ke da yawan jama'a kamar Gaza sai ya karya wannan doka.

To kuma anan ne dokar kaso take shigowa. Saboda me wannan doka ta zama mai mahimmanci? duk lokacin da ya kasance akwai yiwuwar rasa rayukan fararen hula ko kuma lalata dukiyoyinsu, akwai bukatar dogon nazari dan kiyaye hakan.

A wasu lokutan, wannan na nufin abin da tsohon shugaban kotun manyan laiifuka Rosalyn Higgins ya rubuta a wata shari'a - "Koda harin ya zama halastacce amma zai debi kaso mai yawa na rayukan fararen hula da lalata dukuiyarsu, amma ya zama nasara ga dakarun da suka kai harin,".

A ko wanne lokacin za a iya katse duk wani hari da ake shirin kai wa idan aka fuskanci zai jefa fararen hula cikin masifa.

Duk kuma wanda zai kai hari kan kayayyakin soji a wani yanki mai yawan jama'a to sai ya tabbatar da yanayi domin kaucewa kuskure.

Yancin dan Adam

Kotun duniya ta sha nanata cewa ba a watsi da 'yancin dan adam a lokacin yaki, lokacin da ake amfani da wannan doka hakan na nufin bin dokar amfani da makamai kenan a lokacin yaki wadda aka tsara domin shawo kan wasu kalubalen yaki. Abin da hakan ke nufi ba ko yaushe ake kiyayen hakkin dan adam ba ke nan.

Yayin da ake maganar taho mugama a kauyukan Laraba dake Isra'ila, Ba a wani amfani da dokar yaki ta makamai.

Gabashin birnin Kudus cike yake da rudani, saboda lokacin da Isra'ila ke mamaye yankin, duniya na daukar shi a wani bangare na Falasdinawa ciki har da Kotun duniya, wadda ta bayar da shawararta kan cewa a gina katanga da za ta raba yankin Falasdinu a 2004.

Na karshe, shi ne a tuna cewa wannan dokar kawai tana takaita munin ne.