Vous-êtes ici: AccueilActualitésActualités Criminelles2021 05 11Article 450714

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Kenneth Kaunda: Abin da ya sa 'yan Afirka suke mantawa da tarihinsu

Shugaban kasar Zambia na farko Kenneth Kaunda Shugaban kasar Zambia na farko Kenneth Kaunda

Cikin jerin wasikun da muke samu daga 'yan jaridar Afrika, a wannan karon Ade Daramy wanda ruwa biyu ne - dan kasar Saliyo da Gambia - ya yi nazari kan abin da matasan nahiyar ke kallo a matsayin tarihinsu - da kuma abin da ya sa tarihin yake da muhimmanci.

Na yi matukar kaduwa a lokacin bikin murnar cikar shugaban kasar Zambia na farko Kenneth Kaunda shekaru 97, wanda ya yi fafutukar neman 'yancin kasa - na ga da yawan 'yan kasar ba su san shi ba.

Lokacin da na wallafa sakon taya murna ga shugaban a ranar 28 ga watan Afrilu a kafafen sada zumunta, na ce: "Shi ne kadai shugaban Afrika da ya yi mulki a shekarun 1960 wanda har yanzu yake a raye."

Da yawa sun yi ta aika sakon murnarsu. Wasu kuma suna ta mamaki suna cewa: "Au dama yana nan a raye?"

Amma magana ta gaskiya ita ce yawancin 'yan kasa da shekara 30 ba su san shi ba.

Ga wadanda suka girma a shekarun 1960 a Saliyo, abu ne mai wahala su manta da shi.

Ina cikin wata tawagar Afrika ta musamman da ke nazari kan shigowar turawar mulkin mallaka cikin kasashen da suka samu 'yanci a nahiyar.

Firaiministan Birtaniya Harold Macmillan ya ziyarci da yawa daga cikin kasashen da kasarsa ta yi wa mulkin mallaka, ya kuma gabatar da wata fitacciyar makalarsa da ake kira "Gugurwar Sauyi" wato "Wind of Change" a birnin Cape na Afrika ta Kudu a ranar 3 ga watan Fabirairun 1960.

Shekara daya bayan hakan, an bai wa kasashen Afrika 17 'yancin kai.

Ni da abokaina da muke aji daya cikin farin ciki da jin kai muke karanta sunayen shugabannin duka kasashen Afrika ciki har da Milton Margai na Saliyo da Dawda Jawara na Gambia, Jomo Kenyatta na Kenya, Patrice Lumumba na kasar Congo, Ahmed Sekou Touré na Guinea, Modibo Keïta daga Mali, Léopold Senghor daga Senegal - da kuma shi kan shi Mr Kaunda.

Alkawarin kwai da madara

Kaunda, shi ne karami cikin yaran gidansu takwas, kuma malamin makaranta ne gabanin ya shiga gwagwarmayar neman 'yanci.

A lokacin ne aka san shi da yadda yake kada jitarsa, yana kidan wakokin 'yanci kuma yana yin wakar karfafa gwiwa ga yakin neman 'yanci.

Ya zama shugaban kasar Zambia na farko lokacin yana da shekara 40.

Ya ce burinsa kan mutanen Zambia shi ne su rika karin kumallo da kwai da safe, ga madara - kuma ko wa ya zama yana da takalmi a kafarsa.

KK shi ne sunan da aka fi saninsa da shi lokacin shugabancinsa, ya yi matukar shahara kan sukar shugabancin wariyar launin fatar da ake yi a Afrika Ta Kudu da kuma ta gwamnatin farar fata tsiraru a Rhodesia wadda ake kira Zimbabwe a yau - ya kuma bai wa kungiyoyi da suke da irin wannan ra'ayi kuma suke yakar wannan shugabanci kamar irinsu ANC mazauni a Zambia.

Ya kuma fara aiki gadan-gadan domin inganta rayuwar 'yan kasar, sai dai ya ci amanar dimokaraddiya ta hanyar kawo tsarin jam'iyyar siyasa daya tilo a 1973.

Mista Kanda ne kawai dan takara a zaben 1978 da 1983 da kuma na 1987 - inda a duka zabukan yake samun sama da kashi 80 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Zai zamar masa abin kunya a ce ya lashe duka kashi 100.

Har a cikin jam'iyyarsa sai da ya sauya tsarin da zai ba shi dama dan takara daya kacal.

Daga baya mutanen kasar suka kosa da shi suka yi wata zanga-zangar neman a kara jam'iyyu, kuma suka kifar da shi a zaben 1991.

Manta bukatu

Sama da shekara 30, bayan dauki da murnar samun 'yanci, shugabanin mulkin kama-karya ne suka dabaidabaye nahiyar - wanda hakan ka iya zama dalilin da ya matasa ba ma sa iya tunawa da shugabannin farkon ba.

Wasu an yi musu kisan gilla wasu kuma an kashe su wajen juyin mulki, wasu kuma suka manta da bukatun mutanensu da kuma alkawuran da suka yi.

Kuma har yanzu a Afrika akwai shugabannin da suke kan mulki sama da shekara 20 wasu 30.

Wasu ma sun kai shekara 40 kan mulki kamar shugaban kasar Kamaru Paul Biya. Shi ne shugaba na biyu da Kamaru ta taba yi a tarihi tun bayan samun 'yanci daga Faransa 1960.

Hakan yana ba ni mamaki mene ne za a bayyana a tarihin Afrika na yau.

Tun daga nan Mr Kaunda ya hakura da siyasa ya koma gefe ya yi shiru, sai ya mayar da hanakali kan yaki da cutar HIV bayan dansa daya ya mutu sanadinta a karshen shekarun 1980 - mutum ne da bai kamata a manta da shi ba.

Shi ma wani bangare ne da za a rika tunawa da shi a tarihin nahiyar - mai kyau ko mara kyau - kuma za mu iya daukar darasi daga wadannan abubuwan biyu.