Vous-êtes ici: AccueilBusiness2021 03 19Article 449753

BBC Hausa of Friday, 19 March 2021

Source: BBC

'Gyara matatun man Najeriya zai ba da kafar cin hanci'

Gwamnatin ƙasar ta ba da kwangilar ne ga kamfanin Tecnimont mai hedikwata a Italiya Gwamnatin ƙasar ta ba da kwangilar ne ga kamfanin Tecnimont mai hedikwata a Italiya

Masana na ci gaba da tsokaci kan kwangilar da gwamnatin Najeriya ta bayar ta gyara daya daga cikin manyan matatun manta wadda ke birnin Fatakwal a kudancin kasar a kan kudi dala biliyan daya da miliyan dari biyar.

Gwamnatin ƙasar ta ba da kwangilar ne ga kamfanin Tecnimont mai hedikwata a Italiya.

Duk da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashe mafiya arzikin mai a duniya, to amma takan sayo tataccen mai ne daga kasashen waje saboda lalacewar matatunta - kuma ana zargin lamarin na haifar da rashawa da tsadar man ga gwamnati da kuma 'yan kasar.

Dokta Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur a Najeriya ya shaida wa BBC cewa matakin gwamnatin sam ba zai haifar da wani ci gaba ba ganin yadda shekarun baya ma aka dauki irin wannan matakin amma kuma ba a ga wani abin a zo a gani ba.

A cewarsa, yunƙurin gyara matatun man bai zama dole ba saboda akwai mahimman abubuwa da ya kamata a ce gwamnatin ta mayar da hankali a kai domin ci gaban Najeriya.

"A wannan lokaci da duniya ta karkata aƙalarta ta hanyar gwamnati ta cire hannunta a harkar kula da man fetur, sai muka ga Najeriya yanzu ma take ƙara dulmiyar da hannunta a cikin kula da harkar man fetur". in ji masanin.

Dokta Ahmed Adamu ya bayyana cewa zai yi wuya a iya kammala aikin cikin lokacin da aka ɗiba na gudanar da shi.

Ya bayyana cewa yawan gyara tsofaffin matatun man "wata dama ce ga wasu suke amfani da ita domin samun kuɗin shiga ko kuma a yi cin hanci da rashawa".

Yadda aikin gyara matatar man zai amfani Najeriya

A cewar masanin tattalin arzikin man fetur ɗin, matatar man ta Fatakwal, idan za ta yi aiki ɗari bisa ɗari, za ta iya biyan rabin buƙatun man da ƴan Najeriya suke da shi.

Sai dai ya ɗiga ayar tambaya kan yiwuwar ita matatar man ta yi aiki ɗari bisa ɗari ganin cewa tsohuwar matatar mai ce.

Ya kuma ce ko da an gyara matatar man dole ne sai an shigo da man daga wasu ƙasashen amma a ganinsa, gyara matatar zai yi tasiri sosai wajen samar da mai cikin sauƙi a Najeriya tare da rage hauhawar farashin kayan masarufi saboda "mai yana alaƙanta da sauran farashin kayan abubuwa".