Vous-êtes ici: AccueilBusiness2021 03 18Article 449739

BBC Hausa of Thursday, 18 March 2021

Source: BBC

Shugabannin Afrika da suka mutu kan mulki a shekara 20 da suka wuce

Shugaban Tanzania John Magufuli ya rasu ranan Laraba 17 ga watan Maris Shugaban Tanzania John Magufuli ya rasu ranan Laraba 17 ga watan Maris

A ranar Laraba 17 ga watan Maris ne shugaban Tanzania John Pombe Magufuli ya rasu yana da shekara 61 a duniya.

Mataimakiyar Shugaban ƙasar Samia Suluhu ce ta tabbatar da mutuwar shugaban a kafar yaɗa labaran ƙasar.

A cewar mataimakiyar shugaban, Mista Magufuli ya mutu ne da yammacin ranar Laraba a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam sakamakon ciwon zuciya.

Ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar. Saluhu ta ƙara da cewa a ranar 14 ga watan Maris ne jikin shugaban ya yi tsanani inda kuma aka kwantar da shi a asibiti - a nan kuma ya mutu.

BBC ta yi nazari kan shugabannin Afirka da suka mutu cikin shekara 20 da suka wuce.

Daga cikin su dai akwai wadanda suka mutu sakamakon rashin lafiya, yayin da wasu kuma kashe su aka yi.

Ga dai jerin sunayen shugabannin da kasashensu da kuma sanadin mutuwar tasu: