Vous-êtes ici: AccueilBusiness2021 05 16Article 450810

BBC Hausa of Dimanche, 16 Mai 2021

Source: BBC

Matsalar tsaro a Najeriya: Tsohon shugaban Najeriya Babangida ya bukaci a yi wa gwamnatin Buhari addu'a

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya yi nuni da cewa samar wa da sojoji kayan aiki da horo shi ne babban jigon karya lagon matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

A sakonsa na barka da sallah ya bukaci 'yan Najeriya da su bai wa gwamnatin kasar haɗin kai don samar da zaman lafiya da tsaro, yana cewa babbar gudummawar da jama'a za su bayar kenan daga nasu bangaren don ganin an shawo kan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa.

Tsohon shugaban na mulkin soja ya bayyana matsalar tsaro a matsayin babban kalubalen da Najeriya ke fama da shi a halin da ake ciki, a don haka ne ya bukaci jama'a da su tashi tsaye wajen taimaka wa gwamnati da addu'a, da kuma ba ta hadin kai don kawo karshen matsalar.



Latsa lasifikar da ke sama don jin karin bayanin da ya yi wa BBC