Vous-êtes ici: AccueilBusiness2021 05 10Article 450683

BBC Hausa of Monday, 10 May 2021

Source: BBC

Sojojin MDD na Ethiopia 'yan Tigray sun nemi mafaka a Sudan

Hoton was sojojin tabbatar da zaman lafiyar na Habasha a Sudan Hoton was sojojin tabbatar da zaman lafiyar na Habasha a Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da sojojin tabbatar da zaman lafiya da ke karkashinta dari daya daga Habasha sun nemi kariya ta kasa da kasa tare da neman mafaka a Sudan.

Dakarun na daga cikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya da aka rufe ofishinsu kwanan nan a yankin Darfur, na Sudan.

Lamarin ya taso ne bayan da wasu sojojin tabbatar da zaman lafiyar na Habasha, wadanda ainahi suka fito daga yankin Tigray wanda ya yi fama da rikici, suka ki yarda su koma Ethiopiar saboda tsoron gallaza musu.

Ana samun karuwar damuwa a kan zargin cin zarafi da aka aikata a lokacin rikicin wata shida na yankin na Tigray.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce maimakon sojojin tabbatar da zaman lafiyar su koma gida Ethiopa bayan kammala aikinsu a yankin Darfur, dakarun kusan 120 daga Ethiopia sun mika bukatarsu ta neman mafaka a Sudan.

Ana danganta lamarin da irin zaman dar-dar da ake fama da shi na rikicin kabilanci da ya tsananta a Habashar sakamakon tashin hankalin yankin Tigray na arewa.

Ko a watan Fabrairu a kasar Sudan ta Kudu ma wasu sojojin tabbatar da zaman lafiya na Ethiopiar, wadanda ainahi daga yankin Tigray suka fito sun ki komawa kasarsu saboda fargabar za a gallaza musu.

Akwai rahotanni da dama na keta hakkin dan adam a tsawon rikicin da aka yi na wata shida a Tigray.

Rikicin da rahotanni suka ce ya yi sanadiyyar kisan dubban mutane, ya kuma raba kusan mutane miliyan biyu, ko daya bisa uku na yawan al'ummar yankin na Tigray da muhallansu tun lokacin da rikicin ya barke a farkon watan Nuwamba na 2020.

Jama'ar yankin su ne kusan kashi shida cikin dari na al'ummar kasar ta Habasha sama da miliyan 110.

A ranar Asabar shugaban Cocin Gargajiya ta Habasha, wanda shi ma dan kabilar yankin Tigray din ne ya ce abin da aka yi musu, ya kai kisan kiyashi.

Masu fashin baki sun yi kiyasin kafin rikicin, kungiyar TPLF, da ke mulkin yankin sama da shekara talatin, wadda ke fafutukar samun 'yanci daga Ethiopia tana da mayaka wajen dubu 250, wadanda yanzu ba a san nawa ta yi asara ba a rikicin.

Daga cikin manya-manyanta da ta rasa akwai tsohon Ministan Hrkokin waje na Ethiopia Seyoum Mesfin, yayin da tsohon shugaban gwamnatin mulkin yankin na Tigray Abay Weldu, ya shiga hannun gwamnatin tarayya.