Vous-êtes ici: AccueilBusiness2021 05 10Article 450685

BBC Hausa of Monday, 10 May 2021

Source: BBC

Boko Haram: Sojoji sun ce sun kama 'yan Boko Haram 10 a Kano

Rundunar sojojin Najeriya Rundunar sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ta yi ikirarin kama mutanen da suke zargi da kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram a birnin Kano da ke arewa maso yammacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar, Njoko Irabor, wanda ya tabbatar wa BBC hakan, ya ce sun kama mutanen ne a wani masallaci da ke unguwar Hotoro a cikin birnin Kano ranar Asabar.

Ya ce sun kamo mutanen ne a wani samame da suka kai masallacin bayan samun bayanan sirri a kansu.

A cewarsa, suna ci gaba da faɗaɗa binciken da tattara bayanan sirri da zummar inganta tsaro a jihar ta Kano.

Rahotanni sun ce wannan kamen ya tayar da hankulan mazauna wasu yankunan birnin na Kano.

Wannan ne karon farko cikin lokaci mai tsawo da hukumomi suke sanar da kama wadanda ake zargi da kasancewa 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram a jihar Kano.

A shekarun baya, birnin na Kano ya yi fama da hare-hare na mayakan kungiyar, wadanda suka taba tashin bam a babban masallacin da ke kofar gidan Sarkin Kano da kuma wasu wurare.

Rundunar sojin ta kama mutanen ne a yayin da kungiyar Boko Haram ke matsa kai hare-hare musamman a Arewa maso gabashin kasar.

A watan jiya mayakan kungiyar sun hari garin Geidam da ke jihar Yobe inda suka kashe mutanen da dama sannan suka tilasta wa daruruwan mutane tserewa daga gidajensu zuwa wasu garuruwa.

Kazalika mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kafa tuta a wasu kananan hukumomi biyu na jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, kamar yadda gwamnan jihar Sani Bello, ya shaida wa manema labarai a watan jiya.