Vous-êtes ici: AccueilBusiness2021 05 11Article 450706

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Al Khamis da Jum'ah: Ƴan Twitter na fatan a yi azumi 30 a Najeriya

Idan har aka yi azumi 30, kai tsaye Alhamis za ta kasance ranar Sallah a matsayin 1 ga Shawwal Idan har aka yi azumi 30, kai tsaye Alhamis za ta kasance ranar Sallah a matsayin 1 ga Shawwal

Hasashen yin azumi 30 ya ja hankali tare da faranta ran wasu ƴan Najeriya musamman masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter.

Kwamitin ganin wata na Fadar Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar musulmin ƙasar su fara dibon watan Shawwal a ranar Talata da ta kasance 29 ga Ramadan.

Amma kuma kwamitin ya nuna zai yi wahala a iya ganin jinjirin watan ranar Talata.

Batun ranakun hutun da za a yi idan har aka yi azumi 30 shi ne ya ja hankalin ƴan Najeriya a Twitter.

Idan har aka yi azumi 30, kai tsaye Alhamis za ta kasance ranar Sallah a matsayin 1 ga Shawwal.

Don haka gwamnatin Najeriya za ta sanar da Alhamis da Juma'a a matsayin ranakun hutu. Ga kuma hutun ƙarshen mako.

Batun hutun Alhamis da Juma'a ya kasance ɗaya daga cikin wanda aka fi tattaunawa a Najeriya a Twitter, inda mutane kusan 7,000 suka yi tsokaci akai.

Me ake cewa?

Ƴan Najeriya da dama da suka yi tsokaci a Twitter na fatan gara ma a yi azumi 30 don su more hutun kwana huɗu a jere.

Kuma yawancin waɗanda suka yi tsokaci sun haɗa har da musulmi da waɗanda ba musulmi ba da ke fatan a yi azumi 30.

A cewar @Ab_talbah ya fi son a yi azumi 30 don hutu ya faɗo Alhamis da Juma'a ga kuma hutun ƙarshen mako.