Vous-êtes ici: AccueilCultureMusique2021 03 17Article 449695

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Zlatan Ibrahimovic ya yi amai ya lashe

Tawagar kwallon kafa ta Sweden ta bai wa Zlatan Ibrahimovic goron gayyata, bayan shekara biyar da yin ritaya daga buga mata tamaula.

Mai shekara 39 ya ci wa kasar kwallo 62 a wasa 116, daga baya ya yi ritaya bayan da aka fitar da Sweden daga gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2016.

Dan wasan ya bude kofar ci gaba da yi wa kasar tamaula a wata hira da aka yi da shi a wata jarida a Nuwambar 2020, hakan ne ya bai wa koci Janne Andersson damar zuwa Milan inda ya gana da dan kwallon.

Ibrahimovic ya ci kwallo 14 a wasa 14 da ya buga wa AC Milan a kakar bana.

Sweden za ta kara da Georgia ranar Alhamis 25 ga watan Maris, sannan kwana uku tsakani ta fafata da Kosove gida da waje a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a 2022.

Dan kwallon ya fara yi wa Sweden tamaula a lokacin yana da shekara 19 a karawa da tsibirin Faroe, ya kuma fara cin kwallo a karawa da Azerbaijan a 2002 a wasan zuwa gasar kofin duniya.

Sweden ta bai wa Ibrahimovic kyaftin a gasar nahiyar Turai a 2012, wanda ya ci wata kayatacciyar kwallo a karawa da ta ci Faransa 2-0, sai dai a wasannin cikin rukuni aka fitar da kasar.

Tsohon dan wasan Barcelona da Paris St-German da Manchester United da kuma LA Galaxy, wanda ya koma AC Milan kan yarjejeniyar wata shida a Janairun 2020 - yana da yarjejeniyar ci gaba da wasa a Italiya kaka daya.

Ibrahimovic ya ci wa Manchester United kwallo 29 a wasa 53, wadda ta soke kwantiraginsa da shi, daga nan ya koma buga gasar Amurka a kungiyar Galaxy a 2018.