Vous-êtes ici: AccueilSport2021 05 25Article 450942

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Yadda wani ya yi yunƙurin halaka Limamin Masallacin Ka’aba

Wani mutum sanye da harami ya yi yunkurin kashe ɗaya daga cikin limaman Masallacin Ka'aba.

Hukumomin da ke kula da Masallatai biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain sun ce an yi yunƙurin halaka Sheikh Baleelah lokacin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma'a.

Haramain Sharifain ya wallafa bidiyon a shafukansa na sada zumunsa yadda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa ga limamin da kuma yadda jami'an tsaro suka murƙushe shi.

Hukumomin sun ce "mutumin ya tunkari mumbarin limamin ne riƙe da makami a masallacin Ka'aba amma an yi nasarar murƙushe shi."



An taɓa yunƙurin kutsawa da mota cikin Masallacin Ka'aba a guje

An taɓa yunƙurin kutsawa da wata mota cikin Masallacin Ka'aba a guje, inda ta dangane da ƙofar shiga cikin masallacin ta 89.

Lamarin ya faru ne a watan Oktoban 2020 a daren juma'a

Motar ta kunna kai ta Farfajiyar Sarki Fahd, wadda aka haɗe ta da masallacin daga baya.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda motar ta yi awon gaba da shingen kariya sannan ta dangane da ƙofar shiga masallacin.



Sai dai hukumomi sun bayyana cewa babu wanda ya jikkata a hatsarin sannan kuma an kama direban nan take. Wasu hotuna sun nuna yadda aka ɗaure hannayensa kafin a fita da shi.