Vous-êtes ici: AccueilSport2021 05 17Article 450832

BBC Hausa of Lundi, 17 Mai 2021

Source: BBC

Barcelona ta tsira da Copa del Rey a kakar bana

Lionel Messi, kyaftin din Barcelona Lionel Messi, kyaftin din Barcelona

Barcelona ta barar da damar lashe kofin La Liga na bana, a lokacin da gasar ta zo karshe da ake sa ran karkare wasannin ranar Asabar.

Tun bayan da kungiyar ta Camp Nou ta doke Athletic Club ta lashe Copa del Rey na bana, daga lokacin kwazon da take yi a La Liga ya yi kasa har ta kai Granada ta doke ta a Camp Nou.

Cikin wasannin da suka rage mata a bana, Barcelona ita ce ta biyar a kungiyar da ta kasa samun maki masu yawa tare da Athletic a lokacin da ake daf da karkare gasar ta La Liga.

Bayan da Granada ta doke Barcelona, kungiyar ta Camp Nou ta yi nasara a kan Valencia, sannan ta yi canjaras da Atletico Madrid da Levante, sannan ta sha kashi a gida a hannun Celta Vigo ranar Lahadi.

Hakan na nufin Barcelona ta hada maki biyar daga 15 da ya kamata ta samu, sai Osasuna da ta samu maki hudu, Granada da Levente kowacce ta hada maki uku-uku, sannan Real Valladolid mai maki biyu.

Cikin wasannin da suka rage a gasar La Liga, Celta Vigo ce ta yi nasara a karawa biyar, yayin da Real Madrid ta hada maki 11, ita kuwa Atletico maki 10 ta samu.

Karawar karshe da ta rage a gaban Barcelona ita ce da Eibar a wasan karshe a La Liga, kuma kungiyar ta Camp Nou za ta buga fafatawar domin kare martabarta a gasar ta Spaniya.

Barcelona ba ta lashe komai ba a kakar 2019/20, yayin da ta kare a mataki na biyu a kan teburi, inda a bana take ta uku a gasar ta Spaniya.

Wasannin mako na 37 a gasar La Liga:

Ranara Juma'a 21 ga watan Mayu:

  • Levante da Cadiz


Ranar Asabar 22 ga watan Mayu

  • Celta Vigo da Real Betis


  • Osasunada Real Sociedad


  • Real Madrid da Villarreal


  • Real Valladolid da Atletico Madrid


  • Eibar da Barcelona


  • Elche da Athletic Bilbao


  • Huesca da Valencia


Ranar Lahadi 23 ga watan Mayu

  • Granada da Getafe


  • Sevilla da Deportivo Alaves