Vous-êtes ici: AccueilSport2021 03 12Article 579200

BBC Hausa of Friday, 12 March 2021

Source: bbc.com

Kasuwar musayar ƴan ƙwallo: Makomar Aguero, Varane da Ronaldo

Barcelona ta bai wa ɗan wasan gaba na Argentina Sergio Aguero mai shekara 32 kwantiragi wanda kwantiraginsa da Manchester City zai zo ƙarshe a ƙarshen kakar wasan bana. (Tycsports - in Spanish)

Real Madrid za ta saurari tayi kan ɗan wasanta na baya Rapheal Varane a kakar wasan nan. Rahotanni na cewa ɗan wasan na Faransa mai shekara 27 ya nuna sha'awa a wani mataki na son shiga gasar Premier. (AS - in Spanish)

Chelsea na iya sayar da ɗan wasan gaba na Jamus Timo Werner a wannan kakar wasan shekara ɗaya bayan da ɗan wasan mai shekara 25 ya bar ƙungiyar RB Leipzig kan kuɗi £54m. (Football Insider).

Dan wasan gaba na Manchester United Edinson Cavani, mai shekara 34, zai jira har zuwa karshen kakar wasa ta bana kafin ya yanke shawara kan makomarsa, duk da cewa mahaifin dan wasan ɗan ƙasar Uruguay ya nuna yana son sanya ƙulla kwantiragi da Boca Juniors. (ESPN)

Juventus ba ta duba yiyuwar tsawaita wa Cristiano Ronaldo kwantiragi, in ji daraktan wasanni na kungiyar Fabio Paratici. (Express via Sky Italia)

Liverpool kuwa na zawarcin ɗan wasan Santos kuma ɗan Brazil Angelo Gabriel. (Sport Witness)

Newcastle na shirin ƙulla kwantiragi da Mathew Bondwell ɗan wasan baya na Ingila mai buga wa rukunin ƴan kasa da shekara 18 a kyauta bayan ya bar kulob ɗin RB Leipzig. (Telegraph)

Dan wasan gaba na Portugal Eder yana jan hankalin Brighton yayin da ɗan wasan mai shekara 33 yake shirin barin Lokomotiv Moscow a wannan kakar wasan. (A Bola - in Portuguese)

Vous êtes témoin d'un fait, vous avez une information, un scoop ou un sujet d'actualité à diffuser? Envoyez-nous vos infos, photos ou vidéos sur WhatsApp +237 650 531 887 ou par email ! Les meilleurs seront sélectionnés et vérifiés par la rédaction puis publiés sur le site.

Rejoignez notre newsletter