Vous-êtes ici: AccueilSport2021 03 15Article 579798

BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: bbc.com

Grammys 2021: Yadda Burna Boy da Wizkid suka lashe kyautar mawaka

Mawakan Najeriya masu salon kidan Afrobeats Burna Boy da Wizkid sun samu kyautar Grammys ta 2021.

Faifan wakar Burna Boy ya zama na daya a duniyar mawaka yayin da wakar Wizkid ta bidiyo wadda suka yi da Beyonce mai suna Brown Skin Girl ta zama cikin wadanda suka fi kyau a duniya.

'Yar Beyonce Blue Ivy ita ma ta lashe kyauta kan wakar.

An bai wa mai ba da umarni da wanda ya tsara wakar kyautar wakar bidiyon da ta fi ko wacce kyau a wannan shekara.

Karo na biyu kenan a jere ana sanya sunan Burna Boy - wanda sunansa na gaskiya Damini Ogulu - cikin wadanda za su iya samun kyautar Grammys.

A shekarar 2020 an sanya sunansa a cikin masu takara sai dai mawakiya Angelique Kidjo ta yi nasara.

Wannan ne karo na 63 da aka gudanar da bikin ba da kyautar Grammy da ya gudana a birnin Los Angeles na kasar Amurka. Shi ne bikin mawaka mafi girma da ake gudanarwa a duniya, amma na wannan shekarar ya zama na daban saboda annobar korona.

Wakar bidiyon da ta fi ko wacce

Wanda ya lashe: wakar Brown Skin Girl - wadda Beyoncé da 'yarta Blue Ivy da kuma Wizkid suka rera.

Wakokin da suka yi takara

Life is Good - Future Featuring Drake

Lockdown - Anderson Paak

Adore You - Harry Styles

Goliath - Woodkiddeo

Vous êtes témoin d'un fait, vous avez une information, un scoop ou un sujet d'actualité à diffuser? Envoyez-nous vos infos, photos ou vidéos sur WhatsApp +237 650 531 887 ou par email ! Les meilleurs seront sélectionnés et vérifiés par la rédaction puis publiés sur le site.

Rejoignez notre newsletter