Vous-êtes ici: AccueilSport2021 04 26Article 450427

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Iraƙi: Gobara ta kashe masu cutar korona 21 a Bagadaza

Rahotanni na cewa wutar ta kashe a kalla mutane ashirin da uku Rahotanni na cewa wutar ta kashe a kalla mutane ashirin da uku

Gobara ta tashi a wani sashin bada kulawar gaggawa na masu fama da cutar korona marasa a Bagadaza, babban birnin Iraki.

Rahotanni na cewa wutar ta kashe a kalla mutane ashirin da uku tare da jikkata wasu da dama.

An yi ta kokarin tseratar da marasa lafiya yayin gobarar wadda bayanai ke cewa ta tashi ne sakamakon fashewar iskar oxygen.

Wani jami'in hukumar tsaro ta farin kaya ya ce yawancin marasa lafyar da ke wannan sashi sun mutu, saboda cire musu iskar da suke shaka yayin da ake kokarin ceton rayukansu.