Vous-êtes ici: AccueilSport2021 03 16Article 580076

BBC Hausa of Tuesday, 16 March 2021

Source: bbc.com

Barayi sun shiga gidan Di Maria da Marquinhos

Barayi sun shiga gidan 'yan kwallon Paris St Germain, Angel di Maria da kuma Marquinhos ranar Lahadi a lokacin da kungiyar ke karawa da Nantes.

An sauya dan kwallon Argentina, Di Maria a minti na 62 da taka leda, daga nan aka sanar da shi abin da ya faru a gidansa a wasan da aka doke su 2-1.

Sai da barayin suka kammala abin da suka je yi ne iyalansa suka san mai ya faru.

Mai tsaron baya na tawagar Brazil, Marquinhos ya fada cewar an kuma shiga gidan iyayensa ''amma ba wanda aka raunata''.

Wani mai shigar da kara a Nantes ya ce tuni jami'an tsaro da suka kware wajen zakulo masu shiga gidajen yin sata, suka shiga aiki nan take.

Ko a baya ma sune suka yi aikin bankado wadanda suka shiga gidan Di Maria da Mauro Icardi da kuma Sergio Rico a farkon shekarar nan.

Barayi sun taba shiga gidan tsohon dan kwallon Manchester United, Di Maria a shekarar 2015 a Cheshire.

Vous êtes témoin d'un fait, vous avez une information, un scoop ou un sujet d'actualité à diffuser? Envoyez-nous vos infos, photos ou vidéos sur WhatsApp +237 650 531 887 ou par email ! Les meilleurs seront sélectionnés et vérifiés par la rédaction puis publiés sur le site.

Rejoignez notre newsletter