Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 01Article 450524

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Rikicin Somaliya: Jamian tsaro da ke gaba da juna suna fada takaddama kan wa'adin shugaban kasa-

Wasu daga cikin rundunonin sojin ƙasar suna goyon bayan shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed Wasu daga cikin rundunonin sojin ƙasar suna goyon bayan shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed

Faɗa ta ɓarke a Mogadishu babban birnin Somalia, tsakanin bangarori daban-daban na jami'an tsaro.

Rahotanni sun ce an yi amfani da manyan makamai kuma an yi ta harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar.

Wasu daga cikin rundunonin sojin ƙasar suna goyon bayan shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed yayin da wasu ke adawa da shi.

A makon da ya gabata Mista Mohamed - wanda aka fi sani da Farmajo - ya amince da kara wa'adin mulkinsa na shekaru biyu abinda ya janyo ce ce-ku ce. Aikinsa a hukumance ya ƙare a watan Fabrairu.

Kasashen duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka sun soki matakin.

Rahotanni daga Mogadishu a ranar Lahadin sun ce abin da ya fara a matsayin rikicin cikin gida ya bazu zuwa wasu sassan birnin ciki har da yankunan tsakiya.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ce fadan ya kasance ne tsakanin sojojin da ke goyon bayan gwamnati da kuma sojojin da ke goyon bayan 'yan hammaya, amma wasu tsoffin jagorin yaki da shugabannin hauloli su ma suna cikin rikicin.

Ba a bayyana ko akwai wadanda suka jikkata ba.

Shafin yada labarai ta intanet da ke kira Capital Online, ya ce masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun fantsama kan tituna, suna kona tayoyi, sannan sojoji masu tawaye sun kwace iko da wasu sassan arewacin Mogadishu.