Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 21Article 450346

BBC Hausa of Wednesday, 21 April 2021

Source: BBC

Rawar da Idris Deby ya taka a yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi

Shugaba Idris Deby da kasarsa sun taka muhimmiyar rawa a yaki da Boko Haram Shugaba Idris Deby da kasarsa sun taka muhimmiyar rawa a yaki da Boko Haram

Yayin da ake ci gaba da jimamin mutuwar shugaban kasar Chadi Filmashal Idris Deby Itno, za mu yi waiwaye kan irin rawar da ya taka a yaƙi da masu ta da kayar baya na kungiyar Boko Haram.

Ƙungiyar Boko Haram dai ta daɗe tana cin karenta babu babbaka a yankin Tafkin Chadi, inda rikicin ya fi shafar Najeriya, sannan sai Kamaru da Chadi da Nijar.

Tun daga shekarar 2015 a lokacin da kasar Chadi ta shiga ƙawancen yaki da kungiyar Boko Haram, Shugaba Idris Deby da kasarsa sun taka muhimmiyar rawa a yaki da Boko Haram.

A ranar Talata ne rundunar sojin Chadi ta ce Shugaban kasar Idriss Deby ya mutu sakamakon raunukan da ya ji a fagen daga. A halin yanzu dai Chadi tana fafatawa da mayakan da ke tawaye wadanda suka kaddamar da hari kan babban birnin kasar N'Djamena.

Ana sa ran Shugaba Idriss Deby zai lashe zaben shugaban kasar karo na shida bayan zaben da aka gudanar a watan Afrilu.

A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce, Shugaba Idriss Déby na Chadi "ya ja numfashinsa na ƙarshe a yayin da yake kare martabar ƙasar a fagen daga". Tuni dai an rusa gwamnati da majalisar dokoki. Majalisar ƙoli ta soji za ta jagoranci ƙasar har na tsawon wata 18.

Ƙoƙarin yaƙi da Boko Haram

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ma ya bayyana marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da 'jajirtaccen shugaba', wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a yaƙin da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ''babban abokin Najeriya.

"Sannan ya sanya hannu a yakin da kasar ke yi da Boko Haram, wadanda suka haddasa matsalar tsaro ba a Najeriya ba har da kasashen ta makofta musamman ita kan ta kasar Chadi, da Kamaru da jamhuriyar Nijar," in ji sanarwar shugaban.

Barister Audu Bulama Bukarti mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a Afirka, ya kuma ce yankin Sahel na Afirka ba zai taɓa mantawa da marigayi Idris Deby ba a yaƙi da 'yan Boko Haram.

"Idan ba a manta ba har sai da ya turo sojoji a shekarar domin su taya sojojin Najeriya yaƙi da kungiyar, kuma sun taka gagarumar rawa a nan.

"Kasancewar sojojin Chadi jarumai ne, hasalima ana ganin baki dayan Afirka Ta Yamma babu jaruman sojoji kamar su," in ji Barista Bulama.

Ana ganin jarumtarsu ta taka rawa wajen yaƙi da kungiyar da kuma karya lagon Boko Haram a shekarun 2015 da 2016 da kuma 2017.

Wannan ne ya sa a shekarun nan na baya-baya da hadakar Najeriya da Chadi ta samu matsala har shi Shugaba Idris Deby a shekarar 2020 ya ce ba za su ci gaba da yakar kungiyar Boko Haram a wajen Chadi ba.

"Wannan ya kawo matuƙar giɓi a yaƙi da ƙungiyar, ya kuma ba ta damar yin ƙarfi, har ta ci gaba da kai manya-manyan hare-haren da muke gani a shekaru biyun nan da suka gabata,'' in ji Bulama Bukarti.

Gagarumin giɓi a yaƙi da Boko Haram

Bukarti ya ce hakika mutuwarsa za ta bar gagarumin giɓi a yaƙin da ake yi da kungiyar Boko Haram, hakan ka iya ruru wutar rashin zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka Ta Yamma.

''Saboda ita kanta kasar Chadi idan ba a yi a hankali ba za ta ƙara rikicewa, domin siyasa da mulki da sojoji za su ci gaba da haddasa rigingimu.

"Daman wadanda suka kashe shi 'yan tawaye ne, su kuma tun da sun kashe shugaba za su ƙara matsa ƙaimi a kan abubuwan da suke yi. Mutuwar Idris Deby za ta bar giɓi kan rashin yanke hukunci a gwamnati.

Mai sharhin ya ci gaba da cewa idan rikicin siyasar Chadi ya ƙara rincaɓewa to harkar tsaro za ta rikice, idan haka ta faru sojoji za su koma gida ba za su ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin masu jihadi a yankin Tafkin Chadi da ɓangaren Sahel wanda akwai sojojin Chadi a cikinsu ba.

To wannan zai ƙara munana al'mura ba wai a ƙasar kadai ko Tafkin Chadi ba, har ma da yankin Sahel da Afurka ta yamma baki daya.''