Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 23Article 450375

BBC Hausa of Vendredi, 23 Avril 2021

Source: BBC

Aubameyang da Lacazette ba za su yi wasan Everton ba

Pierre-Emerick Aubameyang da kuma Alexandre Lacazette ba za su yi wasan ba, inji manaja Arteta Pierre-Emerick Aubameyang da kuma Alexandre Lacazette ba za su yi wasan ba, inji manaja Arteta

Ranar Juma'a ne Arsenal za ta karbi bakuncin Everton a wasan mako na 33 a gasar Premier League da za su fafata a Emirates.

Sai dai kyaftin din Gunners, Pierre-Emerick Aubameyang da kuma Alexandre Lacazette ba za su yi wasan ba.

Kamar yadda kungiyar ta sanar ta kara da cewar watakila Martin Odegaard ya yi fafatawar ta ranar Juma'a.

Har yanzu Aubameyang bai warke daga maleriya da ya kamu a lokacin da ya je buga wa tawagar Gabon wasa ba, amma ana sa ran zai koma atisaye a karshen makon nan.

Shi kuwa dan wasan tawagar Faransa, Lacazette wanda ya yi rauni a wasan da Arsenal ta tashi 1-1 da Fulham ranar Lahadi, na yin jinya har yanzu.

Arsenal ta kara da cewar mai tsaron baya, David Luiz na murmurewa, tana fatan zai koma atisaye mai dan sauki a mako mai zuwa.

Sannan tana sa ran nan da mako biyu zuwa uku Kieran Tierney zai koma karbar horo, bayan jinyar rauni a gwiwar kafarsa.

Tuni kuma dai dan kwallon tawagar Norway, Odegaard ya ke atisaye mai dan sauki, bayan jinya da ya yi.

Arsenal tana ta tara a kan teburin Premier League da tazarar maki uku tsakaninta da Everton, wadda take ta takwas da kwantan wasa.