Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 15Article 449663

BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: BBC

Mazauna jihar Kano na kokawa kan satar allunan maƙabartu

Ana samun ƙaruwar sace allunnan alamomi na kaburbura Ana samun ƙaruwar sace allunnan alamomi na kaburbura

Masu kula da wata maƙabarta dake Gwale a jihar Kano na ci gaba da kokawa kan irin yadda suka ce ana samun ƙaruwar sace allunnan alamomi na kaburbura.

Masu kula da makabartar sun shaidawa BBC cewa tun kusan watanni uku baya ne suka lura ana yi wa shaidar da ake sakawa ƙaburbura ɗauki ɗai-ɗai, yayin da wasu kuma allunnan suke ganinsu a lanƙwashe idan gari ya waye lamarin dake nuni da cewa an yi ƙoƙarin cirewa ne amma hakan ta gagara.

Wakilin BBC a Kano Khalifa Shehu Dokaji wanda ya je maƙabartar ƙafa da ƙafa, ya ce ya ga kaburbura da dama da aka cire allunansu aka tafi da su, wasu kuma a allunan alamarsu lauye.

Ɗanjuma Labaran na daga cikin masu haƙar kabari a wannan makabarta ta Dandolo, ya kuma bayyanawa BBC cewa tun da farko sun fara samun koke ne daga wajen jama'a. dangane da ɓatan allunan da suka sanya a kabuburan ƴan uwansu da aka binne a wannan maƙabarta.

"Muna zargin ƴan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe su, don sune suke yawo a nan wajen, sukan zo su wuce, kuma akwai gefen makabarta da suke irin waɗannan ayyukan," inji Malam Ɗanjuma.

To sai dai wasu masu sana'ar ta tsince-tsincen kayan ƙarafan wato gwan-gwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.

Jihar Kano dai na da tarin maƙabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewa kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka a ciinsu.

A wasu lokuta a baya, an sha samun waɗanda ke shiga maƙabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu da wata mummunar manufa.

Jihar Kano na da mai bawa gwamna shawara na musamman kan lamuran da suka shafi maƙabartu, amma duk da haka wasu ƴan jihar na kokawa kan yadda ake samun matsaloli irin waɗannan.