Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 18Article 449734

BBC Hausa of Jeudi, 18 Mars 2021

Source: BBC

Guardiola ya sha gaban Mourinho a Champions League

Kocin Man City Pep Guardiola Kocin Man City Pep Guardiola

Ranar Talata Manchester City ta kai zagayen quarter finals a Champions League na bana, bayan da ta doke Borussia Monchengladbach da ci 4-0 gida da waje.

A karawar farko da suka yi a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a wasan da suka kara ranar 24 ga watan Fabrairu, City ce ta yi nasara da ci 2-0.

Da wannan sakamakon Pep Guardiola ya ci wasa 82 a gasar Champions League da ya ja ragamar Barcelona da Bayern Munich da kungiyar Etihad.

Hakan ne kuma ya sa kocin dan Spaniya ya zama na hudu a jerin masu horarwar da suka ci wasanni da dama a gasar ta zakarun Turai.

A baya dai Guardiola da Jose Mourinho na kafada da kafada a mataki na cin wasa 81 kowanne a Champions League, koda yake Mourinho ya ja ragamar karawa 152, Guardiola kuwa 131 ya yi.

Bayan da Guardiola ya haura Mourinho, kalubalen da ke gaban sa, shi ne ya tarar da tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger da yake mataki na uku da Carlo Ancelotti na biyu.

Kowannensu ya ci wasa 90 a Champions League, sai dai Wenger karawa 184 ya ja ragama, yayin da Anceloti ya yi fafatawa 166.

Wanda yake mataki na daya shi ne Sir Alex Ferguson, wanda ya yi nasara a karawa 109 a wasa 190 da ya kai Manchester United a Champions league.