Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 21Article 450344

BBC Hausa of Wednesday, 21 April 2021

Source: BBC

An samu Derek Chauvin da laifi a kisan bakar-fata George Floyd a Amurka

Mutuwar George Floyd ta haifar da barkewar tarzoma a biranen Amurka da dama Mutuwar George Floyd ta haifar da barkewar tarzoma a biranen Amurka da dama

An sami tsohon jami'in ɗan sanda Derek Chauvin da laifi a tuhume-tuhume biyu da ake yi masa a kan kisan gilla da kuma kisa bada gangan ba dangane da mutuwar George Floyd bakar fatar Ba'amurke da ya yi amfani da karfi wajan kama shi a watan Mayun bara.

Sakamakon mai tarihi, a wata kotu da ke Minneapolis, ya zo ne bayan shari'ar makonni uku da ake gani a matsayin wani zakaran gwajin dafi a kan yadda kan 'yan sanda suke aiki, kuma muhimmin lokaci ne a dangantakar da ke tsakanin bakar fata da farar fata.

Mutuwar George Floyd ta haifar da barkewar tarzoma a biranen Amurka da dama da kuma zanga zanga a wasu ƙasashen duniya bayan da Derek Chauvin ya dora gwiwarsa akan wuyarsa fiye da mintuna tara,

A yanzu tsohon jami'in ɗan sandan zai kasance a hannun 'yan sandan har zuwa lokacin da za a yanke masa hukuncin ɗauri a gidan kaso wanda ake ganin zai kai shekara 40 a gidan yari.

Za a yi wa sauran jamian ƴan sanda uku da ke tare da Derek Chauvin shari'a a shekarar da mu ke ciki.