Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 12Article 450749

BBC Hausa of Wednesday, 12 May 2021

Source: BBC

Manchester City ta lashe Premier bayan Man United ta yi ɓari a hannun Leicester

Manchester City ta lashe kofin Premier karo uku cikin shekara huɗu Manchester City ta lashe kofin Premier karo uku cikin shekara huɗu

Manchester City ta lashe kofin Premier karo uku cikin shekara huɗu bayan babbar abokiyar hamayyarta Manchester United ta sha kashi hannun Leicester City.

Pep Guardiola ya lashe kofin ne da tazarar maki 10 kan United da ke matsayi na biyu yayin da ya rage wasa uku a kammala Lig.

Yanzu Guardiola mai shekara 50, ya lashe kofuna takwas tun zuwansa Manchester a 2016.

Tun a ranar Asabar ya kamata City ta lashe kofin amma ta sha kashi hannun Chelsea 2-1 a Etihad Stadium.

Amma yanzu, Leicester ta kammala aikin inda ta doke Manchester United 2-1 a Old Trafford ranar Talata.

Kofi na biyu kenan da City ta lashe cikin mako biyu bayan ta doke Tottenham a kofin Carabao kuma yanzu tana harin lashe kofin zakarun Turai bayan ta kai wasan ƙarshe inda za ta haɗu da Chelsea.