Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 22Article 450358

BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Lewandowski ya koma yin atisaye a Bayern Munich

Robert Lewandowski, dan kwallon Bayern Munich Robert Lewandowski, dan kwallon Bayern Munich

Robert Lewandowski ya koma atisaye a Bayern Munich ranar Laraba, bayan jinyar wata daya da ya yi.

Ranar Asabar ake sa ran Bayern za ta lashe kofin Bundesliga na kuma tara a jere, idan ta doke Mainz a gasar Bundesliga.

Dan kwallon tawagar Poland, mai shekara 32 ya koma atisaye, bayan jinyar raunin da ya yi a gwiwar kafarsa a lokacin da yake buga wa kasarsa tamauala

Tuni kocin Bayern, Hansi Flick ya ce yana fatan Lewandowski zai ci gaba da cin kwallaye, domin kamo tarihin Gerd Muller da ya zura 40 a raga a kakar 1971/72.

Lewandowski wanda ya ke da 35 a raga a kakar bana, kuma saura karawa uku a kammala Bundesliga ta bana ya ce bai sani ba ko zai iya doke tarihin da Muller ya kafa.

Haka kuma Serge Gnabry ya koma karbar horo, bayan da ya kammala killace kansa, sakamakon kamuwa da cutar korona.

Shima Corentin Tolisso ya koma atisaye, bayan jinya da ya yi.