Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 19Article 450871

BBC Hausa of Wednesday, 19 May 2021

Source: BBC

Faransa ta gayyaci Benzema cikin tawagar kwallon kafarta

Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid ta tawaggar Faransa Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid ta tawaggar Faransa

An bayya Karim Benzema cikin 'yan wasan tawagar kwallon kafar Faransa na kwarya-kwarya, domin buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Dan wasan Real Madrid ya yi shekara biyar da rabi rabon da ya buga wa kasarsa tamaula, bayan wani faifan bidiyo na lalata da ake zarginsa da kokarin cin dunduniyar wani dan wasan tawagar.

Mai shekara 33 zai fara yi wa kasar wasa a karon farko tun bayan Oktoban 2015, inda ake sa ran zai buga gurbin masu cin kwallo tare da Kylian Mbappe da kuma Antoine Griezmann,

Benzema wanda ya ci kwallo 21 a wasa 81 da ya buga wa Faransa ya zama gwarzon dan kwallon kasar da ya yi fice a bana da ke taka leda a waje da kungiyar kwararrun 'yan wasan Faransa suka zaba ranar Talata.

Dan wasan wanda ya ci wa Real Madrid kwallo 29 a bana, ya yi bajintar zura kwallo fiye da 20 a kaka uku kenan tun bayan da Cristiano Ronaldo ya bar Santiago Bernabeu ya koma Juventus a 2018.

Faransa za ta fara gasar cin kofin nahiayr Turai da Jamus a Munich ranar 15 ga watan Yuni, kwana hudu tsakani ta fafata da Hungary a Budapest.

Za kuma ta karkare karawa ta uku ta cikin rukuni na shida da Portugal ranar 23 ga watan Yuni.