Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 06Article 449505

BBC Hausa of Saturday, 6 March 2021

Source: BBC

Jamhuriyyar Nijar: An dawo da sadarwar Internet

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Al'ummar Jamhuriyyar Nijar sun wayi gari ranar Asabar din nan da sadarwar Internet, bayan shafe kwana goma sha daya da katseta, sakamakon barkewar tashin hankali bayan zabe.

Cikin wadannan kwanaki harkokin kasuwanci, da mu'amalar al'umar kasar da yan uwansu dake wasu kasashen duniya sun tsaya cik, to amma gwamnati ta ce ta dauki matakin ne da zummar rage kaifin tashin hankalin da ya barke.

Tun a ranar 24 ga watan jiya ne aka datse wa al'ummar kasar layukan intanet a jahohi 8 na fadin kasar baki daya.

Tun dai lokacin da aka yanke layin na intanet a kasar ta Nijar 'yan kasar da dama ke jiran maido da ita, ganin yadda harkokinsu da sauran kasashen duniya suka tsaya ciki.

Ana danganta katsewa sadarwar da zanga-zanga da ta biyo bayan sanar da sakamakon zabe shugaban kasa zagaye na biyu da hukumar zaben kasar wato CENI ta yi.

Hukumar ta sanar da cewa dan takarrar jam'iyar PNDS-Tarrayya Mohamed Bazoum ne ya fi yawan kuri'a a zaben, yayin da 'yan bangaren adawa ke cewa dan takarar jam'iyar RDR -Canji Mahamane Ousmane ne ya yi rinjaye.

Tuni dai dama wata kungiyar matasan lauyoyi ta kasar ta Nijar ta shigar da kara a gaban kotu, tana neman a dawo da Internet a kasar.

Kungiyar ta sanar da cewa yanke intanet ya kasance wata hanya ta keta hakkin dan adam kamar yadda dokokin kasa da kasa kan sadarwa su ka yi tanadi.

Masu sanya ido kan irin abubuwan da ke gudana a kasar ta jamhuriyar Nijar sun ce gwamnatin kasar ce ta bayar da umurni na a yanke layin sadarwar na intanet domin hana watsa labarai irin na tunzuri.

To sai dai duk da rashin sadarwa daga bangaren intanet, ana iya amfani da sadarwar Internet na kamfanoni wato Wifi.

Maido da intanet a kasar ta Nijar a tsakiyar dare, ya sa dalibai da dama fitowa titi domin anfani da internet a yayin da wasu yanzu haka ke ci gaba da yin hira da abokai da aka jima ba a zanta ba.