Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 20Article 450874

BBC Hausa of Thursday, 20 May 2021

Source: BBC

Majalisar Dattawan Najeriya na son a ɗaure duk wanda ya biya kuɗin fansa shekara 15 a gidan yari

Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya

Majalisar Dattawa a Najeriya na son a haramta biya da karɓar kuɗin fansa domin kuɓutar duk wani da aka yi garkuwa da shi.

Haka kuma majalisar ta nemi a yanke wa duk wanda aka kama ya biya ko ya karɓi kuɗin fansa hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari.

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da kudirin na 2021 mai taken 'magance ayyukan ta'addanci kuma sanarwar ofishin shugaban majalisar dattawan ya fitar ta ce kudirin yanzu ya tsallake karatu na biyu.

Idan kudurin ya zama doka, hukuncin biyan kuɗin fansa za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.