Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 18Article 449729

BBC Hausa of Jeudi, 18 Mars 2021

Source: BBC

Ana jimamin rasuwar matar da ta yi wakar 'Mai daraja Annabi Ma'aiki'

Sayyada Rabi'atu Haruna Sayyada Rabi'atu Haruna

Musulmi a Najeriya da ma wasu kasashen duniya sun fada cikin jimamin rasuwar Sayyada Rabi'atu Harun, matar nan da ta yi fice wajen wakokin yabon Annabi Muhammad (SAW).

Mijinta Sharif Mu'az ya shaida wa BBC cewa a ranar Talata ne mawakiyar ta rasu a Rigasa da ke birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan ta yi jinyar mako uku.

Ya ce an yi jana'izarta da yammacin ranar ta Talata.

A cewarsa mutuwar Sayyada Rabi'atu ta yi matukar girgiza shi da iyalinsa yana mai yin addu'ar Allah ya jikanta.

Sharif Mu'az ya bayyana mai dakin nasa a matsayin mutuniyar kirki wadda ya ji dadin zama tare da ita. Sayyada Rabi'atu ta bar 'ya'ya biyu a duniya.

Ta yi wakokin yabon annabi wadanda suka hada da 'Sayyidin Nasi Karimi', 'Mai daraja Annabi Ma'aiki', Zahra'u Fadima, Shukriyya Sajida, da wasu da dama.

Masu sha'awar wakokinta da ma sauran Musulmi musamman a shafukan sada zumunta sun yi matuka kaduwa da jin rasuwar mawakiyar wadda ta bar 'ya'ya uku a duniya.

Isa Usman ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Sayyada Rabi'atu yana mai yin addu'ar Allah Ya sa ta kasance "bakuwar Muhammadur RasululLah Sallallahu Alayhi Wa Sallam."

Shi ma Adamu Aliyu Shu'aibu ya yi mata fatan samun rahamar Allah sannan ya ce yana "kaunar wakokinta irin su 'Na yi dace na rike soyayyar ma'aiki, da 'Abin dogaro Muhammadu' da kuma Karimiya"

A nasa bangaren, Bilya Hamza Dass, ya yi alhini sannan ya bayyana daya daga cikin wakokinta da ya sani.