Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 21Article 450342

BBC Hausa of Wednesday, 21 April 2021

Source: BBC

George Floyd: Muhimman abubuwa biyar game da shari'ar Derek Chauvin

Mutuwar Floyd ya haifar da gagarumar zanga-zanga a fadin duniya game da nuna wariyar launin fata Mutuwar Floyd ya haifar da gagarumar zanga-zanga a fadin duniya game da nuna wariyar launin fata

Mutuwar George Floyd, bakar fata mai shekaru 48, bayan da wani jami'in dan sanda farar fata Derek Chauvin ya makure shi lokacin da aka cafke shi a Minneapolis cikin watan Mayun shekarar 2020, ta girgiza duniya tare da haifar da gagarumar zanga-zanga a fadin duniya game da nuna wariyar launin fata da cin zalin da 'yan sanda ke yi.

Shari'ar Mista Chauvin da aka shafe makonni uku ana yi kan aikata laifin kisan kai ta saurari bahasin shaidu 45 tare da share sa'oi ana kallon bidiyon da mutanen da suka gane wa idansu abin da ya faru.

Yayin da masu taimaka wa alkalin ke nazari game da sakamakon hukuncin, ga muhimman abubuwa biyar game da shari'ar:

1. Tasirin cafkewar shi ga shaidu

An samu wasu bayanai masu karfi a kwanakin farko lokacin da shaidu suka yi bayani kan abin da suka gani a wannan rana.

Darnella, wacce shekaraunta 17 lokacin da aka kashe Mista Floyd, ta nadi faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta a fadin duniya.

Ta shaida wa masu taimaka wa alkalin cewa akwai daren da ta kasa barci ''tana neman afuwar George Floyd saboda rashin yin wani abu da kuma yin wata magana da kuma rashin ceton rayuwarsa.''

"Idan na tuna George Floyd, na kan tuna da mahaifina, na kan tuna da 'yan uwana maza, na kan tuna da kawunni na. Saboda dukanninsu bakaken fata ne,'' in ji ta.

Bayanai masu tayar da hankali kuma sun fito ne daga Charles McMillian, mai shekaru 61, wanda yana daga cikin mutane na farko da suka fara zuwa wurin da lamarin ya faru kuma ya yi kokarin rokon a kyale Mista Floyd ya shiga motar 'yan sandan.

Ya fara zubar da hawaye yayin da yake kallon faifan bidiyon mai tayar da hankali a cikin kotun, yana mai cewa ya kasa tabuka komai yayin da hakan ke faruwa ya kuma bayyana cewa ya fito ya kalubalanci Mista Chauvin bayan da aka dauke Mista Floyd a cikin motar daukar marasa lafiya saboda ''abin da na kalla bai dace ba.''

Masu kare wanda ake tuhuma sun bayyana cewa kasancewar mutunen da ke wurin ya kara harzuka Mista Chauvin zuwa aikata abin da ya yi a ranar.

Kotun ta ji daga bakin jami'in rundunar 'yan sanda ta Minneapolis, Peter Chang, cewa mutanen da ke wurin ''sun rika tunzura jami'an 'yan sandan.''

Nicole McKenzie, wanda ke horar da jami'an 'yan sandan hanyoyin kula da kiwon lafiya, ya ce kasancewar taron jama'ar a lokacin da aka cafke shi ka iya haifar da cikas ga jami'an wajen gano duk wata damuwa da ke tare da duk wani wanda aka tsare.

2. Bayanai masu tayar da hankali daga budurwarsa

Wani abin al'ajabi kuma ya faru a lokacin da budurwar Mista Floyd da suka shafe shekaru uku tare, Courteney Ross, ta zo ta tsaya a gaban alkalai.

Ta bayyana haduwarsu ta farko da shi, a farfajiyar cibiyar kula da wadanda ba su da matsuguni, inda Mista Floyd yake aiki a matsayin mai tsaron wurin, da kuma yadda ya shiga damuwa bayan mutuwar mahaifiyarsa a shekarar 2018.

Miss Ross ta kuma shaida wa kotu cewa dukanninsu biyu sun sha fama ta matsanancin ciwo, da ya haifar musu da yawan shan maganin rage radadin ciwo.

"Mun samu kanmu cikin yawan shan wannan magani da sai da yawa muka yi ta fafutikar ganin mun daina," a cewarta.

Daya daga cikin muhawarar da lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma ke yi shi ne, Mista Floyd ya mutu ne saboda matsalolin da ya samu a sakamakon yawan sha irin wadannan magunguna da kuma sinadarin methamphetamine da ya riga ya ratsa jininsa a lokacin da aka cafke shi.

3. Shin an yarda da amfani da karfin tuwo?

Wani gagarumin batu a cikin shari'ar shi ne ko Derek Chauvin karya dokar murkushewa a lokacin da ya durkusa a kan wuyan George Floyd har na tsawon minti tara da rabi.

Babban jami'in rundunar 'yan sanda na Minneapolis Medaria Arradondo, daya daga cikin manyan shaidu masu gabatar da kara ne kuma ya kori Mista Chauvin kwana guda bayan abkuwar lamarin.

Ya shaida wa zaman kotu cewa ya kamata a ce jami'in dan sandan ya dakata da amfani da karfin a kan wuyan Mista Floyd a lokacin da ya lura ya daina kokawa. "Ba ya cikin horon da muka yi kuma ba ya cikin tsarin mutuntaka da kimar aikinmu" a ci gaba da amfani da irin wannan karfi," in shi .

Shaida kuma lauya mai bayar da kariya Barry Brodd, kwararre a fannin amfani da karfin tuwo, ya ce an yi wa Mista Chauvin uzuri wajen nuna sanin aikinsa saboda ''mummunar barazanar'' da Mista Floyd ya nuna a wajen kokarin kwacewa daga hannun jami'an.

Amma kuma lokacin da yake amsa tambayoyi, ya amince cewa hadarin da ke tattare da makure wuyan mutum - ya kasa numfashi a cikin wani yanayi - sanannen abu ne a tsakanin jami'an tsaro.

4. Musabbabin mutuwar

Musabbabin mutuwar Mista Floyd wani muhimmnin abu ne a wannan shari'ar, yayin da masu gabatar da kara sukatsaya a kan cewa ya mutu ne a sakamakon rashin shakar iska, yayin da kuma lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma suke nuni da cewa Mista Floyd ya mutu ne saboda magungunan kashe zafin ciwo da ya saba sha.

Dakta Martin, wani kwararre a fannin magungunan da suka shafi cutar numfashi ya yi amfani da faifan bidiyo wajen bayyana abin da ya faru da numfashin Mista Floyd a lokacin mintina tara da rabi da yake karkashin gwiwar Mista Chauvin.

Ko da ''wanda ke da koshin lafiya ne, ya samu kansa cikin irin wannan hali, zai iya mutuwa,'' in ji shi.

Wani muhimmin shaida ga lauyoyi masu bayar da kariya, kwararre a fannin kwayoyin halitta, Daid Fowler ya ce kamata ya yi a rarrabe da mutuwar a matsayin abin da ba a gane ba tukuna, a maimakon a matsayin kisan kai saboda akwai bayanai da dama masu cin karo da juna.

Batutuwa masu sarkakiya da suka hada da yawan amfani da magugunan na Mista Floyd da kuma yiwuwar ya shaki iskar gubar ''carbonmonoxide'' da ke fitowa daga cikin salansar motar 'yan sandan, in ji Dakta Fowler.

5. Amfani da gyaran fasalin tsarin mulki na biyar

Jim kadan kafin lauyoyi masu bayar da kariya su kammala nasu bayanan, wanda ake tuhumar Derek Chauvin - ya tabbatarwa da alkalin kotun cewa ba zai bayyana komai ba.

"Zan yi amfani da damar da nake da ita ta gyaran fasalin doka na biyar,'' ya ce yana nuni 'yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi da ya yi shiru saboda tsoron kada ya sa kansa cikin matsala.

Alkalin ya tambaye shi ko shin wannan ra'ayinsa ne ko kuma wani ne ya saka shi yanke wannan shawarar, Mista Chauvin ya bayar da amsar cewa: "Babu wata barazana, mai girma mai shari'a.''

Mista Chauvin bai amince da aikata laifin tuhumar da ake yi masa ba na kisan kai da gangan - wanda zai iya sa ya fuskanci hukuncin daurin shekara 40 - a kan aikata kisan kai.