Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 20Article 450879

BBC Hausa of Jeudi, 20 Mai 2021

Source: BBC

Transfer rumours: Ings, Kane, Sancho, Ramsey, Griezmann, Flick

Danny Ings, dan wasan gaba na Southhampton Danny Ings, dan wasan gaba na Southhampton

Manchester United na yunkurin dauke Danny Ings, dan wasan gaba na Southhampton mai shekara 28 domin Ole Gunnar Solksjaer ya karfafa 'yan gaba na kungiyar. (Telegraph - subscription required)

Chelsea ta ware fam miliyan 80 domin raba Jadon Sancho, dan wasan gefe mai shekara 21 da kungiyarsa ta Borussia Dortmund, sai dai Manchester United ma na bukatarsa. (Sun)

Wasu kungiyoyi a Turai na kokawar daukan golan Manchester United Dean Henderson, mai shekara 24. Kungiyoyin sun hada da Tottenham, Chelsea, Borussia Dortmund da AC Milan. (Sky Sports)

Aaron Ramsey mai shekara 30 na kasar Wales da Juventus ya shiga jerin 'yan wasan da Liverpool ke sha'awar dauka, inji wani rahoto daga Italiya. (Tutto Juve - in Italian)

Chelsea kuwa na son raba Aurelien Tchouameni, dan wasan tsakiya mai shekara 21 da Monaco da kasarsa Faransa. (Goal)

Kocin Bayern Munich mai barin gado, Hans Flick mai shekara 56 na cikin jerin kocin da Barcelona ke duba yiwuwar dauka ya maye gurbin Ronald Koeman. (RAC1 - in Spanish)

Barcelona za ta sayar da Antoine Griezmann domin rage nauyin rashin kudaden shiga da kungiyar ke fama da ita. (Marca)

Griezmann mai shekara 30 na iya komawa kungiyarsa ta da wato Atletico Madrid inda za a yi musayarsa da Joao Felix. (Sport - in Spanish)