Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 07Article 450661

BBC Hausa of Vendredi, 7 Mai 2021

Source: BBC

Makka: Hotunan Hajarul Aswad da Maƙamu Ibrahim da ba a saba gani ba

Annabi da kansa ne ya ɗora Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba da ke kudu maso gabashi Annabi da kansa ne ya ɗora Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba da ke kudu maso gabashi

Hukumar da ke kula da manyan masallatai biyu mafiya daraja a Saudiyya ta fitar da wasu hotunan Baƙin Dutse wato Hajarul Aswad da ke jikin Ka'aba da Maƙamu Ibrahim wanda aka ɗauka da wata fasaha ta musamman.

An kwashe tsawon sa'o'i 60 ana ɗaukar hotunan da gyara su a na'ura mai ƙwaƙwalwa- sama da sa'a bakwai aka kwashe ana ɗaukar hotunan sannan an yi kusan sa'a 50 ana haɗa hotunan da gyarawa a na'ura don su fito da matuƙar inganci.

An yi amfani da wata fasaha da ake kira 'Focus Stacking' da ke iya ɗaukar hotuna da yawa, sai a harhaɗa su a wuri guda su zama hoto guda mai tsananin inganci.

A wannan karon an ɗauki hotunan dutsen kala 1,050 sannan aka yi amfani da fasahar Focus Stacking aka haɗa su a wuri guda don samun hotunan da suka fito da ingancin 49,000 megapixel.

Daga inda dutsen ya ke a jikin Ka'aba ake fara ɗawafi kuma a nan ake kammalawa.

Ɗawafi shi ne kewaye ɗakin Ka'aba sau bakwai a lokacin Hajji da Umrah. Ana kuma yin Ɗawafi na neman lada (Nafila)

Akwai nisan mita ɗaya daga ƙasa zuwa inda Hajarul Aswad ya ke. Dutsen baƙi ne amma yana da jajaja a jikinsa, sannan tsakiyarsa akwai zurfi kamar ƙwarya.

A Musulunci, an yi imanin cewa an sauko da Baƙin Dutse ne daga Aljanna kamar yadda Annabi Muhammadu ya bayyana.

Annabi da kansa ne ya ɗora Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba da ke kudu maso gabashi, kuma dutsen ya ƙunshi ƙananan duwatsu takwas ne manne da juna sannan aka sanya shi cikin wani babban zobe na azurfa don killace shi.

Ana shafe Baƙin Dutse da wani turare na Oud mai tsada da ƙamshi sau biyar a rana.



Maƙamu Ibrahim

Baya ga hotunan Hajarul Aswad, Hukumar ta fitar da hotunan Maƙamu Ibrahim wato dutsen da ke ɗauke da alamar sawun Annabi Ibrahim wanda ya taka a lokacin da yake ginin Ka'aba.

Shi ma an yi anfani da fasahar ta 'Focus Stacking' wajen ɗaukar hotunan.

Shafin Haramain Sharifain ya wallafa hotunan a Twitter tare da bayanin cewa dutsen Maƙamu Ibrahim dutse ne na Aljanna kamar yadda Annabi Muhammadu ya bayyana.



Dutse ne mai kusurwa huɗu da shaidar tafin ƙafafuwan Annabi Ibrahim. Dutsen na da launin fari da baƙi da ruwan ƙwai kuma yana da faɗin sentimita 50.

Maƙamu Ibrahim a gaban Ka'aba yake daga gabas sannan an kewaye shi da wata rumfa mai ruwan zinari.

A bayansa ne ake so a yi sallah raka'a biyu bayan kammala ɗawafi.