Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 23Article 450370

BBC Hausa of Vendredi, 23 Avril 2021

Source: BBC

Ibrahimovic ya tsawaita kwantiragin zama a AC Milan

Zlatan Ibrahimovic Zlatan Ibrahimovic

Zlatan Ibrahimovic ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a AC Milan zuwa kaka daya.

Milan ta ce Ibrahimovic ya amince zai ci gaba da wasa a Italiya, bayan karawa 130 da ya yi wa kungiyar da cin kwallo 84.

Dan wasan tawagar Sweden shi ne kan gaba a ci wa kungiyar kwallo a bana mai 17 a raga a wasa 25 da ya yi a dukkan fafatawa.

Ibrahimovic wanda ya cika shekara 40 a cikin watan Oktoba ya koma Milan a karo na biyu a Janairun 2020, bayan da ya bar LA Galaxy mai buga gasar Amurka ta Major League.

Dan wasan ya ci kwallo 28 a karawa 45 tun komawarsa Italiya da taka leda.

Kwazon da Ibrahimovic ke yi a Milan ya sa tana ta biyu a kan teburin Serie A da tazarar maki 10 tsakaninta da Inter ta daya a teburin gasar bana.

Kawo yanzu saura wasa shida-shida a karkare kakar bana ta Serie A ta Italiya..