Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 07Article 449525

BBC Hausa of Sunday, 7 March 2021

Source: BBC

Amurka da Koriya ta kudu na shirin tunzura Kim Jong-Un

Sojojin Koriya ta Kudu sun ce babu gudu babu ja da baya wajen gudanar da atisayen lokacin bazara da suke yi da sojojin Amurka a mako mai zuwa a yankin na Peninsula, duk da halin da ake ciki na annoba.

Seoul ta bayyana wannan atisayen na kwanaki tara a matsayin "tamkar wani saitin kwamifiyuta da aka riga aka yi''.

Atisayen haɗin gwiwar ya kasance wani abun janyo tashin hankali tsakanin kasar da yar uwarta Koriya ta arewa. wadda ke kallon shi a matsayin tsokanar yaki, kana ana ganin zai janyo martani daga Koriya ta arewa.

An rage karfin atisayen a 'yan shekarun nan yayin tattaunawa da Pyongyang game da shirinta na nukiliya.

Zaman tankiya tsakani kasashen Koriya Ta Kudu da ta Arewa ya ringa fadada cikin 'yan kwanakin nan, wanda kungiyoyin da suka gudu daga Koriya Ta Arewa zuwa ta Kudu da suke tura sakwannin farfaganda suka ringa izawa.

An yi fatan cewa dangantaka tsakanin Koriya Ta Arewa da ta Kudu da kuma babbar kawarta Amurka za ta inganta bayan ganawar da aka yi tsakanin tsohon shugaba Donald Trump da shugaban Koriya Ta Arewa Kim a kan iyakar kasashen na Koriya, sai dai babu wani abin a-zo a-gani da ya biyo baya, kuma tun lokacin lamura sun ci gaba da tabarbarewa.

Ko da a bara, Koriya Ta Kudu da Ta Arewa sun yi musayar wuta a yankin da ya raba kasashen biyu da aka haramta ayyukan soji.

Sojojin Koriya Ta Kudu sun ce wani harbi da Koriya Ta Arewa ta yi ya samu wajen da sojojinta suke gadi a garin Cheorwon da ke kan iyaka.

Ta ce ta mayar da martanin harbin tare da aike gargadi. Sai dai babu rahotannin jikkata.