Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 15Article 450799

BBC Hausa of Samedi, 15 Mai 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sancho, Varane, Salah, Konate, Haaland, Andersen

Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Borussia Dortmund

Wata majiya da ke kusa da Jadon Sancho na Borussia Dortmund mai shekara 21 na da karfin gwuiwa cewa dan wasan dan kasan Ingila zai kammala komawa Manchester United a karshen wannan kakar wasan. Ana sa ran United za ta yi ma sa tayin farko na fam miliyan 65 zuwa 75. (Eurosport)

United na iya amfani da Jesse Lingard, dan wasan gaba mai shekara 28 a matsayin wanda za ayi musayarsa da Sancho. (Sun)

Manchester United na tattaunawa da Raphael Varane, dan wasan baya na Real Madrid. (Manchester Evening News)

United na shirin yi wa Varane tayin fam miliyan 40 a karshen wannan kakar wasan. (Mirror)

Cikin yan wasan da Paris Saint-Germain ke son daukowa su maye gurbin Kylian Mbappe, dan wasan gaba mai shekara 22, akwai Mo Salah na Liverpool. (ESPN)

Shugaban Kungiyar RB Liepzig Oliver Mintzlaff ya tabbatar cewa Ibrahima Konate, dan wasan baya na Faransa, wanda Liverpool ke sha'awar dauka na iya barin kungiyarsa. Ana sa ran sai an biya fam miliyan 34. (Echo)

An ba kocin Chelsea Thomas Tuchel damar daukan Erling Braut Haland na Borussia Dortmund mai shekara 20, ko Romelu Lukaku na Inter Milan mai shekara 28 da haihuwa. (Express)

Dan wasan gaba na Chelsea Christian Pulisic mai shekara 22 ya yi watsi da hasashen da ake yi cewa zai iya barin kungiyar a karshen wannan kakar wasan. (ESPN, via Metro)