Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 20Article 450339

BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Mun kirkiro European Super League don ceto kwallon kafa — Perez

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez Shugaban Real Madrid, Florentino Perez

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya ce sun kirkiro gasar European Super League ne domin ceto kwallon kafa kan tabarbarewar tattalin arziki da ta shiga.

Real tana cikin kungiyoyi 12 daga Turai da suka saka hannu kan gudanar da gasar Turai da za a dunga gabatar da ita a tsakiyar mako.

Perez ya fada cewa suna wannan kokarin ne, saboda matasa ba sa sha'awar tamaula ''saboda karancin nagartattun wasanni''.

''A duk inda aka kawo batun canji, sai ka samu mutane da suke yin adawa,'' kamar yadda ya fada.

Manyan kungiyoyin Ingila shida da suka hada da Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da kuma Tottenham sun amince su shiga sabuwar gasar.

Wannan shirin na shan suka daga mahukuntan kwallon kafa da gwamnatin Burtaniya da hukumar kwallon kafar Turai da kungiyar Lik-Lik da Fifa.

Firai Minista, Boris Johnson ya shirya taro ranar Talata da hukumar kwallon kafar kasar don tattaunawa kan wannan sabuwar gasar ta European Super League.

Haka kuma za a sa ranar wani taron da kungiyoyin Premier 14 da ba sa cikin wannan sabon tsarin da ake son gudanarwa.

Perez ya fada cewar manyan kungiyoyi suna asarar kudi, saboda haka hada babban wasa zai taimaka musu wajen samun kudin shiga mai tsoka.

Sauran kungiyoyin da ke son kafa European Super League sun hada da Real Madrid da Barcelona da Atletico Madrid da Juventus da AC Milan da Inter Milan.