Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 29Article 450483

BBC Hausa of Thursday, 29 April 2021

Source: BBC

Mohamed Abdullahi Mohamed: Shugaban Somalia ya janye shirin tsawaita wa'adin mulkinsa

Shugaban Somalia Farmajo, ya ce ya fasa neman tsawaita mulkinsa da ƙarin shekaru biyu Shugaban Somalia Farmajo, ya ce ya fasa neman tsawaita mulkinsa da ƙarin shekaru biyu

Shugaban Somalia ya dauki matakin kwantar da ƙura a babban birnin ƙasar, Mogadishu, ta hanyar kira domin a gudanar da sabon zaɓe.

Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmajo, ya ce ya fasa neman tsawaita mulkinsa da ƙarin shekaru biyu.

A makon jiya ne ya amince ya ƙara wa'adin mulkin nasa mai cike da ce-ce-ku-ce bayan an samu saɓani game da yadda ya kamata a gudanar da zaɓukan ƙasar.

Hakan ya haifar da taho-mu-gama da rikici a Mogadishu tsakanin abokan adawarsa da jami'an tsaron ƙasar.

Ana fargabar cewa lamarin zai sa Somalia ta koma 'yar gidan-jiya inda za a riƙa tashin hankali tsakanin ƙabilun irin wanda ya yi sanadin kifewar gwamnatin Siad Barre a 1991.

A gefe guda, Firaiminista Mohamed Roble ya yi kira ga fafaren hular da suka tsere daga gidajensu da su koma.

Dakarun da ke biyayya ga shugaban ƙasar da na waɗanda suke adawa da shi sun mamaye yankuna daban-daban na birnin.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tsakanin mutum 60,000 zuwa 100,000 sun tsere daga gidajensu tun daga ranar Lahadi.

An rage yawan dakarun da ke sintiri a babban birnin tun bayan da Shugaba Farmajo ya sanar da janye aniyarsa ta tsawaita mulki da tsakar daren Talata.

Ya ce zai koma kan shirinsa na tun farko inda zai gudanar da zaɓe.

Me ya sa gudanar da zaɓe ke da matuƙar wahala a ƙasar?

Ana gudanar da zaɓukan Somalia cikin wani tsarin mai sarƙaƙiya wanda kuma ba kai-tsaye ba inda shugabannin ƙabilu suke zaɓen 'yan majalisa, waɗanda su kuma suke zaɓar shugaban ƙasa.

Wa'adin mulkin Shugaba Farmajo ya ƙare a watan Fabrairu amma har yanzu ba a gudanar da zaɓe ba saboda rikicin da ake yi a larduna kan yadda za a raba ɗaunin iko - da kuma rikici kan sabuwar hukumar zaɓen ƙasar.

Somalia ta kwashe shekara da shekaru tana cikin rikci sai dai lamura sun soma daidaita tun daga 2012 sakamakon kafa gwamnatin da Majalisar Ɗinkin Duniya take goyon baya, wadda kuma dakarun tsaron ƙungiyar Tarayyar Afirka suke taimakawa.

A ranar Juma'ar da ta gabata Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce rikicin siyasar Somalia yana raba masa hankali wajen fuskantar manyan matsalolin da ƙasar take fama da su, ciki har da annobar korona, mamayar da farin-ɗango suke yi da kuma rikicin masu ikirarin kishin Musulunci.

Mayaƙan Al-Shabab suna ci gaba da iko da yankuna masu girma da ke wajen babban birnin ƙasar, kuma suna yawaita kai hare-hare a Mogadishu.