Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 25Article 449861

BBC Hausa of Jeudi, 25 Mars 2021

Source: BBC

Limaman da za su jagoranci sallar Taraweeh da Tahajjud a masallancin Harami a bana

Labarai wai limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana Labarai wai limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana

Hukumomin Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami da ke birnin Makka a lokacin azumin bana.

Shafin intanet na Haramain Sharifain ya bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana.

Ana sa ran za a fara Azumin wannan shekarar a cikin watan Afirilu mai zuwa.

Har wa yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasulLimamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka gabata.

Babban limamin masallacin Ka'abah Sheikh Abdul Rahman al-Sudais na daga cikin limaman da hukumomin suka ce za su yi jagorancin sallolin.

Ga hotunan limaman da za su ja ragamar sallolin Tarawi da Tuhajjud.