Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 07Article 450657

BBC Hausa of Vendredi, 7 Mai 2021

Source: BBC

Man United ta kai wasan karshe a Europa League

Ole Gunnar Solskjaer, Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, Kocin Manchester United

Manchester United za ta buga wasan karshe da Villareal a gasar Europa League ta bana.

United ta kai wannan matakin ne duk da rashin nasara da ta yi da ci 3-2 a gidan Roma da suka fafata ranar Alhamis.

A makon jiya United ta doke Roma da ci 6-2 a wasan farko na daf da karshe da suka yi a Old Trafford.