Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeSport2021 05 17Article 450826

BBC Hausa of Lundi, 17 Mai 2021

Source: BBC

Kano Pillars ta ci Adamawa United a Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta doke Adamawa United da ci 1-0 a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahad Kano Pillars ta doke Adamawa United da ci 1-0 a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahad

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke Adamawa United da ci 1-0 a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahadi.

Pillars wadda ke buga wasanninta na gida a jihar Kaduna ta zura kwallo a raga ne ta hannun kyaftin, Rabi'u Ali, kuma sauran minti 10 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Pillars ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburi da maki 40 iri daya da na Akwa United wadda take ta daya, bayan da ta ci Dakkada 2-0.

Jumulla wasa tara aka buga a karawa ta 21 a gasar Firimiyar Najeriya ranar Lahadi, wadda aka ci kwallo 13, sannan kungiyoyi hudu suka ci wasa a waje.

Rivers United ta je ta doke Rangers 1-0, Akwa United ta dura biyu a ragar Dakkada, Mountain of Fire ma ta ci 2-0 a gidan Warri Wolves da wanda Nasarawa United ta je ta doke Wikki da ci 2-1.

Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin gida har hudu da suka sha kashi tun bayan mako na 15 a bara da aka yi irin wannan bajintar.

Sakamakon wasannin mako na 21 a gasar Firimiyar Najeriya:

  • Rangers 0-1 Rivers Utd


  • Dakkada 0-2 Akwa Utd


  • Wikki 1-2 Nasarawa Utd


  • Warri Wolves 0-2 MFM FC


  • Sunshine Stars 0-0 Jigawa GS


  • Kano Pillars 1-0 Adamawa Utd


  • Heartland 2-0 Katsina Utd


  • Kwara Utd 2-0 Plateau Utd


  • Lobi 2-0 FC Ifeanyiubah.