Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeGeneral2021 05 24Article 450915

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rice, Kane, Keita, Bertrand, Griezmann, Fernandinho

Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila

Manchester City na son dauko dan wasan gaba na Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27, wanda shugaban Spurs Daniel Levy ya ki amincewa da shi a lokacin musayar 'yan wasa a watan Junairu. (Sunday Mirror)

Dan wasan tsakiya na Naby Keita, mai shekara 26, ya na son barin Liverpool sai dai eja dinsa ya tuntubi Atletico Madrid domin duba yiwuwar komawarsa Spaniya. (AS - in Spanish)

Everton da Juventus na sha'awar rattaba hannu kan kwantiragin dauko dan wasan Manchester United, kuma mai tsaron ragar Argentina Sergio Romero, mai shekara 34, wanda ke son barin Old Trafford bayan kallon hadarin kajin da Ole Gunnar Solskjaer ya yi masa a wannan kakar wasan. (Mail on Sunday)

Manchester United na shirin dauko dan wasan Bayern Munich da Faransa wato Kingsley Coman. (Bild - in German)

Dan wasan gaba na Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha mai shekara 24 ya ce ba zai amince ba ko da wata babbar kungiya za ta bukace shi ciki kuwa har da Arsenal da Everton. (The Face)

Dan wasan gaba na Middlesbrough Ashley Fletcher mai shekara 24, ya amince ya buga gasar Firimiya a Watford, kan yarjejeniyar shekara biyar. (Sun on Sunday)

A bangare guda kuma Crystal Palace ta nuna sha'awar dauko dan wasan tsakiya FC Copenhagen Victor Nelsson mai shekara 22 wanda a baya-bayan nan akai rade-radin zai koma Aston Villa.(Mail on Sunday)

Leicester City su ne kulob na baya-bayan nan da ke rige-rigen dauko mai tsaron baya na Southampton Ryan Bertrand, inda ita ma kungiyar Arsenal da AC Milan ke nuna sha'awar daukar dan wasan mai shekara 31 da kwantiraginsa zai kare da Leicester da bazara. (Talksport)

Da alamaNewcastle United ta fara sanyawa mai tsaron baya Rob Dickie na Queens Park Rangers, an dade ana sanyawa dan wasan mai shekara 25 ido. (Football Insider)

Eja din dan wasan tsakiya na Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez,mai shekara 23, ya gana da masu ruwa da tsaki na kungiyoyin Atletico Madrid da Real Madrid. (Marca)